Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS

Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS

- A yanzu haka manyan shugabannin rundunar sojin Najeriya sun shiga labule

- Taron wanda shugaban hafsan soji, Tukur Buratai ke jagoranta zai tattauna ne kan halin da kasar ke ciki a yanzu

- Ku tuna cewa kasar na fuskantar matsalar tsaro tun bayan da matasa suka fara zanga-zangar EndSARS a sassa daban-daban na kasar

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, manyan janarori da kwamadojin rundunar na cikin ganawa kan barazanar da tsaron kasar ke fuskanta sakamakon zanga-zangar EndSARS.

Jim kadan kafin fara taron, wanda ke gudana a dakin taron soji a hedkwatar rundunar tsaro, Buratai ya soki wasu kungiyoyin kasa-da-kasa da ba a bayyana sunansu ba.

KU KARANTA KUMA: Garin daɗi na nesa: Gwamna Zulum ya rabawa zawarawa N65m a garin Rann

Ya caccaki kungiyoyin ne a kan barazanar da suke yiwa jami’an soji cewa za su haramta masu fita waje bisa zargin take hakkin dan adam, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya bayyana cewa taron zai tattauna tsari da halin da tsaro ke ciki a yanzu a kasar.

Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS
Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

A cewarsa: “Wasu miyagu na mana barazana da yunkurin hana mana fita waje, amma bamu damu ba saboda ya zama dole mu ci gaba da kasancewa a kasar domin inganta ta.

“Karon farko da na fara fita daga kasar nan, ina da shekaru 50 kuma na kai matsayin Janar, don haka ban damu ba na kare sauran rayuwata a nan.”

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

A wani labari na daban, bata gari a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, sun yashe wani rumbun ajiya mallakar hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya (NEMA) a yankin Jabi adali Biu.

Har ila yau, bata garin sun kai farmaki ga rumbun ajiya na masana’antu masu zaman kansu a yankin Idu, babbar birnin tarayya, sun sace kayayyakin abinci.

A yayin mamayar, yan iskan sun sace buhuhuna da dama na kayan abinci, shinkafa, kwalayen madara, galolin man gyada, abincin gwangwabi, kwalayen taliya, da dai sauransu.

Yan bata garin sun sha karfin jami’an yan sanda a wajen. Mafi akasarin barayin sun zo ne da adaidaita sahun da babura domin cika su da kayan da suka sata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng