Magana Ta Fito, Rundunar Yan Sanda Ta Bayyana Dalilin Kama Tsohon Gwamna a Najeriya

Magana Ta Fito, Rundunar Yan Sanda Ta Bayyana Dalilin Kama Tsohon Gwamna a Najeriya

  • Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta yi karin haske kan dalilinta na kama tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha
  • Dakarun yan sanda sun bayyana cewa sun kama Okorocha ne kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi, ƙirƙirar takardun bogi da sojan gona
  • Ana zargin lamarin ya shafi wata takarda kan zaɓen fitar da gwani na sanatan APC a jihar Imo, wanda Gwamna Hope Uzodinma ya samu nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha tare da bincikarss kafin ta sallame shi a Abuja

Rundunar ta ce kama Okorochia na da alaƙa da zargin haɗa baki wajen aikata laifi, ƙirƙirar takardun bogi da sojan gona a wata takardar korafi kan zaben fitar da gwanin APC na sanata a Imo.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun lallaba otel sun kama tsohon gwamna a Najeriya

Okorocha.
Tsohon gwamnan jihar Imo kuma jigo a jam'iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha Hoto: Rochas Okorocha
Source: Facebook

Yadda aka kama Rochas Okorocha a Abuja

Leadership ta ruwaito cewa yan sanda sun kama Okorocha ne a daren ranar Litinin a otal ɗin REIZ Continental da ke Abuja, bayan zargin kin amsa gayyatar da aka yi masa a baya dangane da lamarin.

Mai magana da yawun rundunar, Aniete Iniedu, ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels, inda ya ce an saki tsohon gwamnan bisa beli bayan an yi masa tambayoyi na kusan awa ɗaya.

Iniedu ya ce an umarci Okorocha da ya koma hedikwatar rundunar yan sanda da ke Abuja ranar Talata domin ci gaba da yi masa tambayoyi yayin da bincike kan zarge-zargen ke gudana.

Rikicin zaɓen fitar da gwanin APC

Kamen ya biyo bayan takaddama kan zaɓen fitar da gwani na APC na kujerar sanatan Imo ta Yamma, inda aka ayyana Gwamna Hope Uzodimma a matsayin wanda ya yi nasara.

Jam’iyyar ta gudanar da zaɓen ne ranar 18 ga Mayu. Sakamakon farko ya nuna cewa Uzodimma ya samu ƙuri’u 230,464, yayin da Okorocha ya samu ƙuri’u 1,098.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Sai dai daga baya wata takarda dabam ta bayyana, wadda ta nuna cewa Okorocha ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 150,780. Wannan ya jawo tambayoyi kan sahihanci da kuma asalin takardar da ake takaddama a kanta.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta hannun ofishinta na jihar Imo, ta shigar da ƙorafi ga Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) da rundunar ’yan sanda dangane da takardar.

Sufetan sanda.
Sufeto janar na rundunar yan sandan Najeriya, IGP Tunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

A cikin wasiƙun da aka rubuta ranar 5 da 8 ga Oktoba, an ruwaito cewa INEC ta bayyana takardar da ta nuna Okorocha a matsayin wanda ya yi nasara da cewa ba ta da sahihanci, tare da buƙatar hukumomin tsaro su binciki asalinta da ingancinta.

An kuma ruwaito cewa INEC ta haɗa kwafin rahoton hukuma da takardar da ake takaddama a kanta cikin ƙorafe-ƙorafen da ta miƙa domin taimakawa binciken.

The Cable ta ruwaito cewa rundunar ’yan sanda ba ta bayyana cikakken bayanin hujjojin da take da su kan Okorocha ko takamaiman yanayin zarge-zargen da ake masa ba.

Yan sanda sun hana taron TMG

Kun ji cewa dakarun yan sanda sun hana taron yan tafiyar "Tinubu Must Go," wanda ak shirya yi a wani wurin taro mai zaman kanta a Kano.

Abba Hikima, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar Tinubu Must Go, ya ce ’yan sanda sun hana su shiga wurin da suka tanada domin taro a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262