Yadda Trump Ya Ajiye Takama Ya Tafi Rasha Neman Agajin Putin
- Shugaban Amurka Donald Trump ya godewa Shugaban Rasha Vladimir Putin bayan sanar da cewa Rasha za ta gaggauta wadatar da Amurka da tan 300,000 na dizal
- Ma'aikatar Tsaron Amurka ta fitar da lasisin wucin gadi don karɓar dizal daga Rasha duk da takunkumin da aka kakaba mata
- Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya soki matakin, inda ya bayyana shi a matsayin "kyauta" ga Putin kuma ya faɗakar da cewa sauƙaƙa matsa lamba ba zai haifar da zaman lafiya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Mambobin jam'iyyar Republican da na Democrat sun haɗu a ranar Juma'a wajen sukar Shugaba Donald Trump sakamakon janye takunkumin da ya yi kan man dizal ɗin Rasha.
Sun kuma bukaci ya yi watsi a shirin watsa hukuncin kisa kai tsaye na tsohon kwamandan sojan da ya kai harin Fort Hood a shekarar 2009.

Source: Getty Images
CGT News ta rahoto Sanata Chris Van Hollen, ɗan jam'iyyar Democrat daga Maryland, ya mayar da martani da cewa
"Trump ya haifar da yaƙin banza da ya kara farashin dizal. Yanzu kuma yana son ba Putin kudi ya cigaba da yaki ta hanyar seyen dizal daga gare shi. Wannan wani babban kuskure ne."
An soki Donald Trump kan alaka da Rasha
Bayan Hollen, dan majalisar wakilai Don Bacon, ɗan jam'iyyar Republican daga Nebraska, ya ƙara da cewa:
"Kaso 70 na Amurkawa suna goyon bayan Ukraine. Tallafa wa tattalin arzikin Putin kuskure ne yayin da yake amfani da kuɗin wajen rusa birane. Tsare-tsaren shugaban ƙasa kan Rasha da Ukraine ba su dace ba."
Haka zalika, Sanata Elizabeth Warren ta bayyana sanarwar a matsayin "abin kunya," inda ta ce Trump zai iya rage farashin mai ne ta hanyar ƙare yaƙinsa da Iran, maimakon taimakawa wajen samar wa Putin kuɗi.
Tare da sauran abokan aikinta na Democrat, Jeanne Shaheen da Chuck Schumer, sun fitar da sanarwar cewa matakin na sanar da damar sayen dizal ɗin Rasha na tsawon wata shida cin amana ne ga Ukraine.

Source: Getty Images
Ɗan majalisar wakilai Michael McCaul ma ya nuna damuwarsa cewa janye takunkumin zai ƙara ɗaukar nauyin yaƙin Rasha ne kawai.
Haka kuma Sanata Sheldon Whitehouse da ɗan majalisa Don Beyer sun soki yarjejeniyar da cewa Amurka tana ba Rasha kuɗin da za a yi amfani da su wajen kashe 'yan Ukraine ba tare da wani dalili ba.
Magana kan kashe Hasan
Dangane da shirin watsa hukuncin kisa na mai laifin harin Fort Hood, Sanata Mark Warner ya bayyana cewa:
"Harin Fort Hood ya kasance mummunan aiki na tarzoma da ya ci rayukan mutane 13 ba tare da hakki ba. Sai dai akwai bambanci tsakanin aiwatar da hukunci na shari'a da kuma maida shi wata harka ta kallo ga jama'a."
Ya ƙara da cewa aiwatar da hukuncin kisa a fili alama ce ta ra'ayin mulkin kama-karya irin su Iran da Koriya ta Arewa.
Baya bayanin da Trump ya yi a bidiyon da Sky News ta wallafa a X:
An dakatar da kai hari Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ba za ta kai hari kan Iran ba kafin zaɓen majalisar dokokin kasar ba.
Trump ce tattaunawar da suke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana tafiya cikin nasara, saboda haka ba za a kai wa Iran hari ba kafin zaɓen ranar 3 ga Nuwamba.
Yaƙin da aka fara tsakanin Amurka da Isra'ila a kan Iran ya taimaka wajen sa farashin mai ya tashi sama, lamarin da ya haifar da damuwa matuƙa ga 'yan ƙasar Amurka.
Asali: Legit.ng


