Cikakken tarihin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam

Cikakken tarihin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam

A cikin makon da ya gabata ne aka cika shekara 12 da kashe bajimin Malamin nan na addinin Musulunci watau Ja’afar Mahmud Adam. Wasu ‘Yan bindiga ne dai su ka buda masa wuta a Ranar Juma’a yana tsakiyar limancin sallar Asuba.

Wannan Malami ya kware musamman a bangaren Al-Qur’ani na Tafsirinsa da kuma sanin ilmin sa da kira’o’in sa da kuma dalilan saukar ayoyin ciki. Malamin ya karantar da al’umma a Kano, Maiduguri, Kaduna, Katsina da kuma Bauchi.

Wani daga cikin masu bibiyar shafin mu mai suna Nasir Kasim Fulatan daga Kano ya kawo mana tarihin wannan Malami kamar yadda mu ka tsakurowa masu karanta labaran na mu a irin wannan lokaci.

Cikakken tarihin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam
An kashe Sheikh Jafar Mahmud Adam yana da shekaru 45 a Duniya
Asali: UGC

1. Haihuwa da fara neman ilmi

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ne a garin Daura, a farkon shekarun 1960s. Marigayi Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu a Daura, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari “Koza” da ke Arewa da Daura a jihar Katsina. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami a 1971 sai ya zauna a makarantar Malam Abdullahi a cikin Fagge.

Dama can Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani maigirma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malamin ya haddace Alkur'ani ne sai ya ga bukatar ya samu ilmin Boko don haka ya fara karatun zamani a 1980.

Har wa yau, Malam Ja’afar ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar Boko ta manya watau “Adult Evening Classes.”

A 1983 ne Malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na Boko da Arabiya, wanda daga nan ya samu shiga shiga makarantar GATC Gwale a 1984, har ya kammala a1988. Bayan shekara guda ne ya wuce Jami’ar Musulunci ta Madina.

A wannan babbar jami'ar musulunci ta Madinah ne Malamin ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. A wancan lokaci ne aka soma jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin Garin Maiduguri.

Bayan nan Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan. Kafin rasuwar Malamin, yayi nisa wajen karatunsa na PhD) a Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto.

KU KARANTA: Takaitacen tarihin Marigayi Mai shari'a Mamman Nasir

2. Malaman Marigayi Jafar Mahmud Adam

Kamar yadda Malamin ya fada daga cikin malamansa na ilimin addinin Musulunci, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago da ke cikin Kano.

A wajen Malam Dandago ne Marigayin ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi. Sauran Malaman sun hada da Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab.

Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Har yanzu wannan babban Malami na Hadisi Ahmad Ibrahim yana nan da ran sa.

Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt da sauran su.

3. Karatu da darusan da Malam ya koyar a rayuwarsa

Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma. Ja’afar Adam ya sauke Al-Qur’ani kusan sau 2 a Masallacin Muhammad Indimi da ke cikin Garin Maiduguri a jihar Borno, a cikin shekaru barkatai.

Malam ya kuma karantar da Kitabuttauhiid na Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, da kuma littatafan hadisai na Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith. Sauran darusa sun hada da wani littafin tauhidi da ya fice mai suna Kashfusshubuhaat.

Haka kuma Malam ya karantar da litaffin nan na Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, da kuma Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy na Muhammad NasirudDeen Albany.

KU KARANTA: Sarki Sanusi II ya fadawa Gwamnati hanyar maganin zaman banza

4. Almajirai

Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi'u Umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah Usman Gadon Kaya da Malam Usman Sani Haruna da kuma Malam Ibrahim Abdullahi Sani.

Sauran manyan Almajiran Marigayin sun hada da Malam Ali Yunus Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da kuma Malam Anas Muhammad Madabo.

Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).

Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (daidai da 13/04/2007). Malamin ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan an yi masa kisan gilla.

Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi. Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan Aljannatul-firdaus.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng