Musulmi Sun Yi Rashi: Malamin Musulunci Ya Rasu a Adamawa bayan Fama da Jinya

Musulmi Sun Yi Rashi: Malamin Musulunci Ya Rasu a Adamawa bayan Fama da Jinya

  • An sanar da rasuwar wani malamin Musulunci a jihar wanda ya bayar da gudummawa ga addini matuka
  • An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a safiyar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, bayan gajeriyar rashin lafiya
  • An a gudanar da sallar jana’izarsa a yau Juma’a, a Masallacin Dodore da ke Yola, da ƙarfe 4:00 na yamma bayan sallar La’asar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - An shiga cikin alhini bayan sanar da rasuwar malamin addinin Musulunci a jihar Adamawa.

An sanar da rasuwar Modibbo Abubakar Bobboi Modibbo Iya Wuro Yombe, wanda ya bar duniya a safiyar yau bayan gajeriyar rashin lafiya.

Malamin Musulunci ya rasu a Adamawa
Marigayi Modibbo Abubakar Iya ya rasu a jihar Adamawa. Hoto: Mohammed Bashir Buba.
Source: Facebook

Wani Muhammad Bashir Buba ne ya tabbatar da rasuwar malamin a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 9 ga watan Oktobar 2026.

Kara karanta wannan

Umarnin da yan sanda suka ba yan adawa kan ziyarar matar Tinubu a Najeriya

Sakataren majalisar Shari'a ta Najeriya ya rasu

Wannan babban rashi na zuwa ne kwanaki uku kacal bayan jimamin rasuwar wani daga cikin wadanda suka ba addinin Musulunci gudunmawa.

Babban Magatakardar Majalisar Koli ta Tabbatar da Shari’a a Najeriya, Malam Nafi’u Baba Ahmad, ya rasu da safiyar Talata.

An sanar da rasuwar malami kuma lauya a yau Talata, inda aka bayyana cewa za a yi jana’izarsa da karfe 1:30 na rana a Abuja.

Rasuwarsa ta jefa al’ummar Musulmi cikin jimami, musamman wadanda suka san ayyukansa a fannin ilimi, Shari’a da kare muradun Musulman Najeriya.

Yaushe aka sallar jana'izar marigayin a Adamawa?

Sanarwar ta ce an gudanar da sallar jana’izarsa a yau Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, a Masallacin Dodore da ke Yola, da ƙarfe 4:00 na yamma, nan take bayan kammala sallar La’asar.

Kafin rasuwarsa, Modibbo Abubakar Iya shi ne mataimakin shugaban farko na Majalisar Musulmi ta Jihar Adamawa, reshen Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu.

Kara karanta wannan

2027: Arewa ta shirya gagarumin gangamin tallata Tinubu da Shettima

Kuma ya kasance jagora na Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta Yola ta Kudu, shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Musulmi ta Yola ta Kudu, da mataimakin limamin farko na Masallacin Juma’a na Dodore.

Mutane da dama sun yi jimamin rasuwarsa inda suka yi addu'ar Allah ya jiƙansa da rahama, ya sanya shi cikin bayinsa salihai, ya haskaka kabarinsa.

Mutane da dama sun yi jimamin rasuwarsa inda suka yi addu'ar Allah ya jiƙansa da rahama, ya sanya shi cikin bayinsa salihai, ya haskaka kabarinsa.

Katsina: Yan bindiga sun kashe hafizin Kur'ani

Mun ba ku labarin cewa an kashe Umar Sa'ad Moba, ɗalibin makarantar Zam-Zam da ke Kano, bayan wasu masu garkuwa da mutane sun sace shi tare da neman kuɗin fansa.

Hukumar makarantar ta tabbatar da rasuwar ɗalibin, inda ta ce an samu labarin mutuwarsa ne bayan an biya kuɗin fansar da masu garkuwar suka nema.

Umar, ɗan asalin Jibiya a Jihar Katsina, yana ajin karshe kuma yana cikin ɗaliban da makarantar ke alfahari da su, inda ya kasance ɗaya daga cikin jagorori.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.