Aminu Ado Bayero Ya Fita da Jama'arsa a Kano bayan Hana Hawa Doki

Aminu Ado Bayero Ya Fita da Jama'arsa a Kano bayan Hana Hawa Doki

  • Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gudanar da ziyara ta musamman zuwa unguwar Yakasai a yammacin Alhamis domin halartar taron saukar Al-Qur'ani
  • Rahoto ya nuna cewa masoya da 'yan uwa sun tarbe shi a fadar Nassarawa kafin rakiya zuwa wurin taron sa'an nan suka koma tare cikin lumana
  • Wannan Ziyara tana zuwa ne biyo bayan tattaunawar da sarki ya yi da Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano kan kiyaye zaman lafiya da amfani da dawakai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ziyarci unguwar Yakasai da ke cikin birnin Kano a yammacin ranar Alhamis domin halartar wani muhimmin taro na saukar Al-Qur'ani mai girma.

Taron da aka yi wa laƙabi da "Fatahu Yakasai 2.0" ya tara masoya da al'umma da dama waɗanda suka hallara a fadar sarkin da ke Nassarawa da ƙarfe 3:30 na yamma domin yi wa sarkin rakiya zuwa unguwar ta Yakasai.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

Aminu Ado Bayero
Mai martaba Aminu Ado Bayero lokacin tafiya Yakasai. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai game da ziyarar sarkin ne a wani sako da shafin Masarautar Kano ya wallafa a Facebook.

Halartar sarkin zuwa wannan taro na zuwa ne bayan tattaunawar da aka yi tsakaninsa da Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, kan muhimmancin kiyaye tsaro da zaman lafiya a jihar.

Mai martaba Aminu Ado ya fita ba dawakai

Yayin wannan fitowa da ziyara da sarkin ya kai domin taron saukar Al-Qur'anin a Yakasai, ba a ga alamun amfani da dawakai ko gudanar da hawan doki ba yayin da yake tare da masoyansa.

A sanarwar da aka fitar zuwa taron, fadar sarkin ta ce:

"Ana kira ga dukkan masoya Mai Martaba Sarki da su fito domin rakiyar Mai Martaba cikin nutsuwa, tsari, ladabi da biyayya, domin tabbatar da gudanar da wannan taro cikin lumana da kwanciyar hankali."

Aminu Ado ya gana da 'yan sanda

Ziyarar ta Kwamishinan 'Yan Sanda Ibrahim Bakori zuwa fadar Nassarawa na daga cikin matakan diflomasiyya da rundunar ke ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya biyo bayan rikicin sarautar Kano da ya samo asali tun watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An ceto matasa 'yan NYSC da yan bindiga suka sace a Najeriya

Gwamnatin jihar Kano ta rushe masarautu biyar tare da maida Muhammadu Sanusi II matsayin sarkin Kano na 16, sai dai Aminu Ado Bayero ya ƙalubalanci wannan mataki inda yake ci gaba da zama a fadar Nassarawa.

Aminu Ado Bayero
Aminu Ado Bayero a fadar shi. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Wannan yanayi ya jawo shari'u da dama a kotu tare da sanya rundunar 'yan sanda ƙara jajircewa wajen hana duk wani abu da zai iya tayar da ƙura a jihar.

An jaddada dokar hawa doki

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sake jaddada dokar hana hawan doki ko dabbobi a fadin jihar, tare da gargadin cewa za a kama duk wanda ya gudanar da hakan.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ibrahim Adamu-Bakori, ya bayar da wannan gargadi ne yayin wani taron manema labarai a birnin Kano.

Ya ƙara da cewa dalilan da suka sa aka kafa dokar suna nan daram, don haka duk wata ƙungiya ko mutum mai son gudanar da wani taro na hawan doki a fili dole ne ya mika bukatar hakan a rubuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng