Yadda aka Tono Gawar Basarake a Kano bayan 'Yan Bindiga Sun Kashe Shi
- Wasu ’yan bindiga sun sace dagacin ƙauyen Aujarawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, daga gidansa, kafin daga bisani a gano gawarsa
- ’Yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa, amma bayan tattaunawa sun rage zuwa Naira miliyan 50, kafin iyalansa suka yi tayin Naira miliyan 5
- Ɗan marigayin ya yi kira ga gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su kamo waɗanda suka kashe mahaifinsa domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Wasu ’yan bindiga sun sace tare da kashe dagacin ƙauyen Aujarawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, bayan sun kutsa gidansa da misalin ƙarfe 1:30 na dare ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026.
Maharan sun yi harbe-harbe kafin su shiga gidan, inda suka ɗaure wasu ’yan uwa da ke barci a wani ɗaki, sannan suka fitar da dagacin daga ɗakinsa suka tafi da shi.

Source: Original
’Yan bindigar sun nemi N200m
Daily Trust ta wallafa cewa dan uwan marigayin, Muhammad Auwal, ya ce maharan sun yi wa babban ɗan’uwansa duka a cikin gida a gaban iyalansa kafin su tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Auwal ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun kira iyalansa a ranar 18 ga Satumba, inda suka nemi Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa.
Ya ce bayan doguwar tattaunawa, sun rage kuɗin zuwa Naira miliyan 50, amma iyalan suka bayyana cewa ba za su iya biyan wannan kuɗi ba.
A ƙarshe, a ranar 22 ga Satumba, iyalan sun yi tayin biyan Naira miliyan 5, suna fatan masu garkuwar za su amince su saki dagacin. Sai dai, a cewarsa, masu garkuwar sun daina kiransu.
An gano gawarsa bayan kwana 13
Auwal ya ce iyalan ba su sake samun labari daga masu garkuwar ko ’yan sanda ba sai ranar 30 ga Satumba, lokacin da suka ji an gano gawa a Danladin, Gezawa.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Ya bayyana cewa lokacin da suka je wurin, an sanar da su cewa ’yan sanda sun bayar da umarnin birne gawar. Daga nan suka je ofishin ’yan sanda domin neman bayani.
Auwal ya ce an nuna musu hotunan gawar, inda ya gane ɗan’uwansa ta fuskarsa da ƙafafunsa. Bayan sun kammala takardun da aka bukata a hedikwatar ’yan sanda, aka ba su izinin tono gawar.

Source: Facebook
'Yan uwan marigayin sun tono gawar basaraken tare da yi masa jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci a wannan rana.
An kama dan siyasa a Yobe
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Operation Hadin Kai sun kama wani ɗan siyasar Yobe, Alhaji Wakiil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, kan zargin tallafa wa ’yan ƙungiyar ISWAP.
Rahotanni sun ce an kama shi ne bayan zargin yunƙurin ba jami’an sojoji cin hanci domin a saki wasu waɗanda aka kama kan zargin harkokin samar da kayayyakin tallafi ga ’yan ta’adda.
An ce kamen ya biyo bayan wani bincike da ya haɗa da kwamandan sojoji, domin gano alaƙar da ake zargin ɗan siyasar na da ita da ƙungiyoyin ta’addanci.
Asali: Legit.ng
