Umarnin da Yan Sanda Suka ba Yan Adawa kan Ziyarar Matar Tinubu a Najeriya
- Rundunar ’yan sandan Nasarawa ta bukaci jam’iyyun adawa su sauya ranar tarukansu da aka shirya gudanarwa 10 ga Oktoba
- Ana sa ran matar shugaban ƙasa za ta halarci gangamin APC a Lafia domin ƙarfafa goyon bayan Bola Tinubu da Kashim Shettima
- Yan sanda sun ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaro, hana rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta shawarci jam’iyyun siyasa na adawa da sauran ƙungiyoyin siyasa su sauya ranar gudanar da gangaminsu.
Rundunar ta bukaci shirin da aka tsara yi a ranar 10 ga Oktoba, 2026 da a fasa saboda ziyarar uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a jihar.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Ramhan Nansel, ya fitar a shafinsa na Facebook.
Gangamin da aka shirya wa Tinubu, Shettima
Jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiya ta ware ranar 10 ga Oktoba domin gudanar da babban gangami a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, cewar Daily Trust.
Ana shirya gangamin ne ƙarƙashin ƙungiyar North-Central Grassroots Mobilisation Network, domin tattara goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen shekarar 2027.
Wannan mataki ya biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki na APC a Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Abuja.
Gargadin da yan sanda suka yi
Rundunar ’yan sandan ta ce ana sa ran uwargidan shugaban ƙasa za ta halarci gangamin APC na North Central Grassroots Mobilisation Movement, wanda za a gudanar ranar Asabar.
Ta ce ta roƙi dukkan jam’iyyun siyasa su ɗage duk wani taron siyasa ko gangamin da suka shirya gudanarwa a wannan rana zuwa wani lokaci na gaba.
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da isasshen tsaro, hana yiwuwar arangama tsakanin magoya bayan jam’iyyu daban-daban da kuma hana bata-gari yin amfani da ayyukan siyasa wajen tayar da hankali.
Rundunar ta ce sauya ranar zai kuma taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar uwargidan shugaban ƙasa da sauran manyan baƙin da ake sa ran za su halarci taron, tare da bai wa hukumomin tsaro damar tsara ayyukansu yadda ya kamata da tabbatar da zaman lafiya.
Ta ce ta amince da mutunta haƙƙin kundin tsarin mulki da dukkan jam’iyyun siyasa suke da shi na haɗuwa, gudanar da taron lumana da shiga harkokin siyasa, amma ta bukaci masu ruwa da tsaki su ba da haɗin kai domin kare lafiyar jama’a.
Gwamnatin Tinubu za ta rage farashin mai
A wani labarin, an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a sayar da fetur mai rahusa a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30.
Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele ya ce masu motocin jigilar jama’a za su samu fifiko wajen cin gajiyar rangwamen.
Gwamnati ta kuma ce za a samu sabon tsarin farashin sauke fetur wanda za a rika duba shi duk wata.
Asali: Legit.ng

