'Yan Bindiga Sun Kashe Hafizin Kur'ani Dan Makarantar Sheikh Daurawa

'Yan Bindiga Sun Kashe Hafizin Kur'ani Dan Makarantar Sheikh Daurawa

  • An kashe Umar Sa'ad Moba, ɗalibin makarantar Zam-Zam da ke Kano, bayan wasu masu garkuwa da mutane sun sace shi tare da neman kuɗin fansa
  • Hukumar makarantar ta tabbatar da rasuwar ɗalibin, inda ta ce an samu labarin mutuwarsa ne bayan an biya kuɗin fansar da masu garkuwar suka nema
  • Umar, ɗan asalin Jibiya a Jihar Katsina, yana ajin karshe kuma yana cikin ɗaliban da makarantar ke alfahari da su, inda ya kasance ɗaya daga cikin jagorori

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Hukumar makarantar Zam-Zam da ke Kano ta tabbatar da rasuwar wani ɗalibinta mai suna Umar Sa'ad Moba, bayan masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shi.

Hukumar makarantar ta bayyana hakan ne a cikin saƙon ta'aziyya da ta aikewa iyayen ɗalibin, ’yan uwansa, malamai da sauran waɗanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

A karshe, kotu ta ba da belin matasa da ke tsare kan sanya rigar 'Tinubu Must Go'

Umar Sa'ad Moba
Umar Sa'ad Moba da ya rasu. Hoto: Zam-Zam Islamic College
Source: Facebook

Masu garkuwa sun kashe ɗalibin

A cewar sanarwar makarantar da ta fitar a Facebook, an yi ta neman addu'a a baya bayan masu garkuwa da mutane sun sace Umar tare da neman kuɗin fansa domin su sake shi.

Hukumar ta ce bayan an biya kuɗin fansar da aka nema, sai aka tabbatar da cewa ya mutu a hannun masu garkuwar.

Sai dai sanarwar makarantar ba ta bayyana adadin kuɗin fansar da aka biya ba ko kuma lokacin da aka kashe Umar.

Umar yana SS3 a Zam-Zam

Umar Sa'ad Moba ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Jibiya ce ta Jihar Katsina, kuma yana shekarar ƙarshe ta karatunsa, wato SS3, a Zam-Zam da ke Kano.

Makarantar ta bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin ɗaliban da ake alfahari da su, inda ya kasance cikin jagororin ƙungiyar Da'awa ta kwalejin.

A cikin saƙon ta'aziyyar, hukumar makarantar ta roƙi Allah Ya jiƙan Umar, Ya gafarta masa, sannan Ya bai wa iyayensa, ’yan uwansa, malamansa da abokansa haƙurin rashin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa mace mai ciki da jariri ta'addanci a Kaduna

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An yi Allah wadai da kisan

Wani mutum, Ahmad Usman da ya yi karin bayani a Facebook kan lamarin ya yi ikirarin cewa an biya masu garkuwar Naira miliyan 70 kafin daga bisani aka samu labarin kashe ɗalibin.

Sai dai wannan ikirarin na kuɗin fansa da aka ambata a shafukan sada zumunta ba a tabbatar da shi daga wata hukuma mai zaman kanta ba.

An sace mutane a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata mace mai juna biyu, wani mutum, matarsa da kuma jaririnsu mai wata shida a Alrahus da ke Millennium City, Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, inda maharan suka rika shiga gidaje ɗaya bayan ɗaya suna neman mutanen da za su yi garkuwa da su.

Mijin matar mai juna biyun, Abdulladir Bello, ya ce yana Abuja lokacin da matarsa ta kira shi tana sanar da shi cewa wasu mutane na ƙoƙarin tilasta shiga gidansu, kafin daga bisani ya tuntubi jami’an tsaro kuma sojoji suka tura jami’ansu yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng