Zance Ya Kare: Yadda Atiku Zai Dawo da Tallafin Man Fetur a Najeriya
- Atiku Abubakar ya yi alƙawarin sake duba yarjejeniyoyin da suka shafi ɗanyen man Najeriya domin samar da mai ga matatun cikin gida
- Daraktan yaɗa manufofin yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, ya ce za a fara amfani da ɗanyen man da ake da shi yayin da ake nazarin yarjejeniyoyin
- Shaibu bai bayyana yarjejeniyoyin da za a sake dubawa ba, yawan man da za a iya samu ko yadda za a kare haƙƙin masu ba da rance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce zai sake duba yarjejeniyoyin da ake da su kan samar da ɗanyen mai, ciki har da waɗanda aka kulla domin karɓar rance.
Ya ce matakin zai taimaka wajen samar da isasshen ɗanyen mai ga matatun man fetur na cikin gida, a wani sabon tsarin tallafin man fetur da ya tsara bisa yawan man da ake samarwa.

Source: Facebook
Daraktan yaɗa manufofin yaƙin neman zaɓen Atiku kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ne ya bayyana shirin a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV a shirin The Morning Brief.
Atiku ya bayyana wannan shiri ne a matsayin wani ɓangare na manufofinsa idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Za a sake duba yarjejeniyoyin ɗanyen mai
Phrank Shaibu ya ce sake duba yarjejeniyoyin zai ba gwamnati damar samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida a farashi mai rahusa.
Ya bayyana cewa an riga an yi alƙawarin bai wa wasu ɓangarori ɗanyen man Najeriya domin tabbatar da samun lamuni.
“An jinginar da yawancin ɗanyen manmu domin karɓar rance, kuma an yi wasu yarjejeniyoyi makamantan haka. Za a sake duba mafi yawansu,” in ji shi.
Yadda za a fara aiwatar da shirin
An tambayi Shaibu yadda za a samar da kuɗin gudanar da tsarin tallafin da Atiku ya gabatar, la’akari da yarjejeniyoyin da Najeriya ta riga ta kulla kan ɗanyen mai da kuma buƙatun matatun cikin gida.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin
A martaninsa, ya ce za a iya sake nazarin wasu daga cikin yarjejeniyoyin da aka kulla a baya domin a samu damar amfani da ɗanyen man wajen aiwatar da shirin.
"Za a sake duba wasu daga cikin yarjejeniyoyin da aka yi a baya. Ba wai dole ne a ci gaba da bin su yadda suke ba.” In ji shi.
Shaibu ya ƙara da cewa gwamnati za ta fara amfani da ɗanyen man da ake da shi a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da nazarin yarjejeniyoyin.
“Za mu fara da wanda ake da shi, yayin da ake gudanar da bitar yarjejeniyoyin. Duk abin da muka samu damar dawo da shi, za mu saka shi cikin adadin ɗanyen man da za a yi amfani da shi wajen gudanar da wannan shiri,” in ji shi.
Abubuwan da ba a fayyace ba
Sai dai Shaibu bai bayyana takamaiman yarjejeniyoyin da gwamnatin Atiku za ta sake dubawa ba idan ya zama shugaban ƙasa.
Haka kuma, bai yi ƙiyasi kan yawan ɗanyen man da za a iya dawo da shi domin amfani da matatun cikin gida ba.
Har ila yau, bai yi bayani kan yadda gwamnatin za ta magance batun haƙƙin masu ba da rance da sauran ɓangarorin da suka kulla yarjejeniyoyi da Najeriya ba.

Source: Twitter
Atiku na tattaunawa da Makinde
A wani labarin kuma, kun ji cewa wakilan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gudanar da tarurruka da dama.
Wakilan Atiku da Makinde sun gudanar da tarurrukan ne tare da samun matsaya kan yiwuwar haɗa kai domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng

