'A Shake Masu Wuya Su Mutu,' Za a Rataye 'Yan Fashin da aka Kama a Gombe
- Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa Buhari Sule da Muktari Ali Hilami hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin fashi da makami da kisan kai
- Kotun ta same su da laifin haɗa baki wajen aikata laifi, fashi da makami da kuma kisan kai bayan an gurfanar da su kan kisan Murtala Rabi’u mai shekaru 35
- Alƙalin kotun ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da zargin da ake yi wa mutanen biyu ba tare da wata shakka ba, lamarin da ya kai ga yanke musu hukuncin kisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda fashi da makami da kisan wani mutum.
Alƙali Muhammad-Auwal Haruna ne ya yanke hukuncin kan Buhari Sule da Muktari Ali Hilami bayan kotun ta same su da laifin haɗa baki wajen aikata laifi, fashi da makami da kuma kisan kai.

Source: Facebook
An kashe Murtala Rabi’u a Akko
Punch ta wallafa cewa an gurfanar da mutanen biyu ne bisa zargin hannu a harin da aka kai wa Murtala Rabi’u a ranar 18 ga Satumba, 2025, a ƙauyen Garin Galadima da ke kusa da Pindiga, a ƙaramar hukumar Akko ta jihar Gombe.
Mai gabatar da ƙara, Abdulkadir Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa mutanen sun haɗa baki tare da ɗaukar makamai kafin su kai wa marigayin hari.
Ya ce sun yi amfani da abubuwa masu haɗari, ciki har da sanduna da fartanya, inda suka yi wa Rabi’u rauni mai tsanani wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwarsa.
Laifin da 'yan fashin suka yi
Masu gabatar da ƙara sun ce bayan harin, mutanen sun kwace wayar Rabi’u kirar Itel da ba ta da katin SIM, tare da N7,400.
Lauyan gwamnati ya ce bayan sun kwashe kuɗin, mutanen sun raba shi tsakaninsu kafin su jefar da gawar Rabi’u a cikin gonar masara.
Tribune ta wallafa cewa ya ce laifukan da ake tuhumar mutanen da su sun saɓa wa sassa na 97, 297 da 221 na dokar Penal Code ta jihar.

Source: Original
Za a rataye 'yan fashi a Gombe
Da yake yanke hukunci, Alƙali Haruna ya ce kotun ta yi nazari sosai kan tuhume-tuhumen da aka gabatar, bayanan shaidu da kuma bayanan da ɓangaren kariya ya gabatar.
Alƙalin ya ce:
“Kotun ta duba dukkan tuhume-tuhumen da masu gabatar da ƙara suka kawo, shaidun da aka gabatar da kuma bayanan da ɓangaren kariya ya bayar.”
Ya ce masu gabatar da ƙara sun yi nasarar tabbatar da laifuffukan da ake zargin mutanen da su ba tare da wata shakka ba, musamman bisa bayanan da shaida ta farko ta bayar.
Alƙalin ya ƙara da cewa mutanen biyu sun kasa kafa wata hujjar kariya da za ta wanke su daga tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Kotun ta same su da laifi sannan ta yanke wa Buhari Sule da Muktari Ali Hilami hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Alƙali Haruna ya bayar da umarnin cewa a rataye kowannensu ta wuya har sai ya mutu.
An kashe matar aure a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama mutane biyu da ake zargi da hannu a fashi da makami da kashe matar wani jami’in ’yan sanda a Gombe.
Waɗanda ake zargin su ne Muhammad Bashir Sale, mai shekaru 20 da Musa Sale Ahmad, mai shekaru 18, wanda aka fi sani da “Abba”.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:35 na asuba, lokacin da wasu mutane ɗauke da adduna da wuƙaƙe suka kutsa gidan Inspector Salisu Waziri.
Asali: Legit.ng


