Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Sake Magana kan Zargin Kisan Kiristoci
- Majalisar koli ta addinin Musuunci ta sake yin magana kan zargin kisan kiyashi kan Kiristoci tana mai cewa rashin tsaro ya shafi kowa
- Majalisar karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ta goyi bayan gyaran tsarin tsaro da ‘yan sanda masu cin gashin kansu
- NSCIA ta kuma bukaci gwamnati ta rage tsadar abinci da sufuri, tare da kira ga Musulmai su mallaki NIN da PVC, su shiga harkokin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta yi watsi da ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci ko wata ƙungiyar addini kisan kiyashi a Najeriya.
Majalisar ta ce matsalar rashin tsaro tana shafar dukkan ’yan Najeriya ba tare da la’akari da addininsu ba, don haka bai kamata a karkatar da ita ba.

Source: Twitter
Ta kuma goyi bayan cikakken garambawul ga tsarin tsaron ƙasar, ciki har da tsarin ’yan sanda masu cin gashin kansu idan aka tanadi ƙa’idoji masu kyau, cewar The Nation.
Majalisar ta yi magana kan tsaro
Majalisar ta ce dole ne tsarin ya kasance bisa ƙwarewa, tanadin kundin tsarin mulki, ɗaukar alhaki, isasshen kuɗi da kuma mutunta haƙƙoƙin ɗan Adam.
Waɗannan na daga cikin ƙudurin babban taron NSCIA da aka gudanar a ranar 1 ga Oktoba a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
An gudanar da taron ne karkashin taken “Musulman Najeriya da Muhimmancin Gina Ƙasa”, kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ne ya jagoranta.
Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, manyan limamai, malaman addinin Musulunci da shugabannin manyan ƙungiyoyin Musulmi.
A cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmi da Sakatare-Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, suka sanya wa hannu, majalisar ta ce maganar kisan kiyashin addini na yaudara ce.
Ta ce irin wannan batu na iya ƙara rura wutar tashin hankali da haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin al’ummar Najeriya.
Majalisar ta bukaci Musulmai su ƙi amfani da Musulunci wajen haifar da ƙiyayya da tashin hankali, tare da tabbatar da bayanai kafin yaɗa su.
Ta kuma bukaci malamai su warware duk wata saɓani da ke tsakaninsu ta hanyoyin cikin gida, maimakon barin rikice-rikicen su ƙara ta’azzara.
NSCIA ta ce tsarin ’yan sanda masu cin gashin kansu zai iya ƙarfafa tsaron ƙasar idan aka tsara shi kuma aka daidaita shi tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.
Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta ƙara ƙoƙarin rage tsadar abinci da sufuri, tana mai cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki.
Ta ce hakan na faruwa ne duk da matakan garambawul da gwamnati ke aiwatarwa domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, cewar Punch.
NSCIA ta kuma yi kira da a kare haƙƙin mata da ’yan mata Musulmai na sanya hijabi a makarantu, wuraren aiki da kuma tsakanin masu yi wa ƙasa hidima.
Ta kuma buƙaci hukumomin tsaro su mutunta haƙƙin Musulmai na sanya hijabi yayin gudanar da ayyukansu, tare da kiyaye tanadin doka.
Majalisar ta musamman roƙi Jami’ar Ibadan, Jami’ar Obafemi Awolowo da Jami’ar Legas su bi hukuncin Kotun Ƙoli kan haƙƙin sanya hijabi.
Ta ce hukuncin ya shafi makarantun ƙasa da ƙasa da ke ƙarƙashin waɗannan jami’o’i, inda Musulmai ke da damar sanya hijabi bisa doka.
NSCIA ta kuma roƙi gwamnatin Rivers da shugabancin Jami’ar Jihar Rivers su aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan damar Musulmai su samu masallaci a jami’ar.
Majalisar ta sake tabbatar da cewa Musulunci ya daɗe yana wanzuwa a ƙasar Igbo, tana mai ƙaryata ikirarin cewa Musulmai ba ’yan asalin yankin ba ne.
Sultan ya magantu kan tilasta shiga Musulunci
Mun ba ku labarin cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ba za a tilasta wa kowa shiga Musulunci ba.
Ya bukaci Musulmi su mutunta hakkoki da ’yancin mabiyan sauran addinai, yana mai gargadi kan tilasta wa wani canza addini.
Majalisar NSCIA ta kuma bukaci a bunkasa ilimin addini da na zamani tare da kara wakilcin Musulmi a harkokin kasa.
Asali: Legit.ng


