Kurunkus: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Takardar Murabus din Nafiu Bala daga ADC

Kurunkus: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Takardar Murabus din Nafiu Bala daga ADC

  • Mai Shari’a Peter Lifu ya yi hukunci kan takardae da ɓangaren ADC karkashin David Mark ya dogara da ita wajen tabbatar da murabus ɗin Nafiu Bala
  • Kotun ta gano babban bambanci tsakanin sa hannun da ke takardar da kuma sa hannun Nafiu Bala a takardun shaidarsa
  • Alƙalin ya bayyana cewa tabbatar da ingancin kwafin takarda ba ya nufin an tabbatar da sahihancin sa hannun wanda aka jingina wa takardar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da wata takardar murabus da ake zargin tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa, Nafiu Bala, ya rubuta.

Kotun ta yanke cewa ba a tabbatar da sahihancin takardae ba, don haka ba za a iya amfani da ita a matsayin hujjar cewa Nafiu Bala ya yi murabus daga muƙaminsa a jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

"Abin da Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su duba wajen yanke masa hukunci a zaben 2027"

Kotu ta yi hukunci kan murabus din Nafiu Bala
Nafiu Bala Gombe a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: Nafiu Bala Gombe
Source: Facebook

Kotu ta ƙi amincewa da wasiƙar murabus ɗin

Mai Shari’a Peter Lifu ne ya bayyana hakan a hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, 5 ga Nuwamban 2026, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Takardae ce ɓangaren ADC karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ya dogara da ita wajen nuna cewa Bala ya yi murabus daga muƙaminsa.

Sai dai a sahihin kwafin hukuncin kotun da jaridar The Punch ta samu ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026, lƙalin ya bayyana cewa bincikensa kan sa hannun da ke wasiƙar ya nuna bambanci da sa hannun Nafiu Bala a wasu takardun shaidarsa.

Alƙali ya gano bambanci a sa hannun Nafiu

Mai Shari’a Lifu ya ce ya kwatanta sa hannun da ke wasiƙar murabus ɗin da waɗanda ke cikin takardun shaidar da Nafiu Bala ya rattaba wa hannu a gaban kotu.

Ya bayyana cewa akwai muhimman bambance-bambance tsakanin sa hannun da ke wasiƙar da sauran waɗanda aka amince da su a matsayin na Bala.

Kara karanta wannan

"Karya suke yi": Tinubu ya sake magana kan dawo da tallafin man fetur

Saboda haka, kotun ta ƙi amincewa da wasiƙar a matsayin sahihiyar hujjar cewa Nafiu Bala ya miƙa murabus da kansa.

Alƙalin ya kuma jaddada cewa kasancewar wata takarda tana da sahihin tabbacin kwafi ba ya tabbatar kai tsaye cewa sa hannun da ke cikinta na mutumin da aka jingina wa takardar ne.

A cewarsa, kotu na da alhakin duba irin wannan takarda tare da sauran hujjoji kafin yanke hukunci kan sahihancinta.

Kotun ta bayyana yadda ake tantance sa hannu

Mai Shari’a Lifu ya ce:

“Kasancewar an tabbatar da sahihancin kwafin wata takarda, hakan kaɗai ba ya warware sahihin ƙalubalen da aka gabatar kan ko mutumin da aka ambata a cikinta ne ya sanya hannu a kanta.
“Tabbatar da kwafin takarda na iya nuna cewa kwafin ya yi daidai da takardar da ke hannun hukumar da ta tabbatar da shi. Amma hakan ba lallai ya tabbatar da sahihancin sa hannun da ake takaddama a kai ba.
“Saboda haka, dole ne kotu ta yi la’akari da takardar tare da sauran hujjojin da suka dace.”

Kara karanta wannan

"Ana kewar Buhari": Amaechi ya tuna rayuwa a lokacin tsohon shugaban kasa

Kotu ta yi hukunci kan Nafiu Bala
Nafiu Bala Gombe a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: Nafiu Bala Gombe
Source: Facebook

Nafiu Bala ya soki Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nafiu Bala da ke ikirarin zama shugaban wani ɓangare na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), ya yi zargi kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Nafiu Bala ya zargi Atiku Abubakar da yin watsi da bin doka ta hanyar ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa duk da hukuncin kotu kan rikicin shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng