Yadda Masu Bankin Wema za Su Samu Tallafin N50,000 na NERSI
- Gwamnatin tarayya ta samar da lambar USSD da abokan cinikin bankin Wema za su yi amfani da ita wajen duba cancantar samun N50,000 na NERSI
- An bayyana cewa ana iya duba cancantar tare da amincewa da karbar kudin ta wayar hannu ba tare da bukatar amfani da intanet ba
- Sai dai bude asusun Wema ko ALAT ba ya nufin mutum ya cancanci tallafin, domin gwamnati ce ke tantance wadanda za su amfana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bullo da wata hanya da abokan cinikin Wema Bank za su iya amfani da ita wajen duba ko an zabe su cikin wadanda za su amfana da tallafin N50,000 na shirin NERSI.
Shirin, wanda Ma’aikatar Jin Kai da Rage Talauci ta Tarayya ke gudanarwa, an kirkiro shi ne domin taimaka wa gidaje masu karamin karfi da wadanda ke cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar rayuwa.

Source: UGC
Bayanai da ke shafin NERSI na gwamnati sun nuna cewa abokan cinikin Wema Bank za su iya duba matsayinsu ta lambar USSD da kuma amincewa da karbar kudin.
Yadda za a duba cancanta da Wema
Masu aiki da bankin Wema za su iya bin wadannan matakai domin tantance ko sun cancanci tallafin:
1. Danna lambar USSD: A kira lambar *945*23# ta layin wayar da aka hada da asusun bankin Wema.
2. Duba cancanta: A zabi bangaren duba cancanta, sannan a bi umarnin da wayar za ta bayar.
3. Amincewa da tallafin: Idan mutum ya samu damar cin gajiyar shirin, zai bi umarnin da aka bayar domin amincewa da karbar N50,000.
4. Karbar kudin: Za a kunna asusun wayar wanda za a tura kudin tallafin zuwa cikinsa.
5. Tabbatar da biya: Za a aika wa wanda ya amfana da sakon SMS domin sanar da shi cewa an tura masa kudin.

Source: Facebook
Wadanda za a ba tallafin
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa shirin ya shafi gidaje masu karamin karfi da kuma wadanda ke cikin mawuyacin hali.
Ana tantance wadanda za su amfana ne ta amfani da sahihan bayanan katin shaidar zama dan kasa da kuma rajistar gidaje masu karamin karfi ta kasa.
Shirin ya shafi masu karamin karfi a dukkan shiyyoyin Najeriya shida. Sai dai ba duk mai asusun Wema ne zai samu tallafin ba, domin kasancewar mutum abokin cinikin bankin ba shi kadai ne sharadin cancanta ba.
Yadda masu MTN za su samu kudin
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta bullo da shirin NERSI domin tallafa wa gidaje masu rauni a Najeriya wajen biyan bukatun yau da kullum sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.
An tsara tantance wadanda za su amfana da shirin ne ta amfani da sahihan bayanan katin shaidar zama dan kasa domin gano gidajen da suka cancanci tallafin.
Rahoto ya nuna cewa masu amfani da layin MTN da aka ware wa MoMo PSB kuma za su iya amfani da lambar *671*0# wajen duba matsayinsu.
Asali: Legit.ng

