Gwamna Ya Ji Korafin Musulmi, Zai Gina Masallaci kusa da Gidan Abubakar Malami

Gwamna Ya Ji Korafin Musulmi, Zai Gina Masallaci kusa da Gidan Abubakar Malami

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da sayen wani gida domin mayar da masallacin wucin gadi zuwa na dindindin
  • An sayi gidan ne a yankin Go-Slow da ke Birnin Kebbi, kusa da gidan dangin Abubakar Malami, tsohon ministan shari’a
  • Matasa sun yabawa matakin, inda suka roki gwamnan ya gina masallaci da makarantar Islamiyya domin yaransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da sayen wani gida domin mayar da wani masallacin wucin gadi da ke yankin Go-Slow Road.

Yankin yana Birnin Kebbi, kusa da gidan dangin Abubakar Malami, SAN, wanda shi ne ɗan takarar ADC na gwamnan Kebbi.

Gwamna zai gina wa Musulmi masallaci
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi. Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu.
Source: Facebook

Gwamna zai gina wa Musulmi masallaci

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin addini, Mallam Imrana Bin-Usman, ne ya bayyana hakan yayin miƙa takardar gidan ga mazauna yankin, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Yakin Biyafara: Gwamnati ta tuno zancen kisan gillar da aka yi shekaru 59 da suka wuce

Bin-Usman ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne bayan mazauna yankin sun nemi a samar musu da wurin ibada na dindindin.

Ya ce buƙatar ta biyo bayan sanya fitilun hasken rana da gwamnatin jihar ta yi a kan titunan yankin domin inganta tsaro.

Ya ce gwamnan ya saurari koken mazauna yankin, sannan ya bayar da umarnin sayen gidan domin mayar da masallacin wucin gadi can.

Bin-Usman ya ce wannan mataki tarihi ne, domin ba da jimawa ba gwamnatin ta samar da fitilun hasken rana a yankin.

Ya ce bayan an kammala aikin, mazauna yankin sun bayyana bukatarsu ta mayar da masallacin wucin gadi zuwa wurin ibada na dindindin.

Gwamna ya faranta wa Musulmi bayan samar da masu da masallaci
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Jagoran matasan yankin, Mallam Taslim Tukur-Kola, ya bayyana matakin gwamnan a matsayin abin farin ciki da zai kawo sauƙi ga mazauna.

Ya ce mazauna yankin sun yaba da shawarar gwamnan na magance matsalar rashin ingantaccen wurin ibada na dindindin.

Tukur-Kola ya ce yankin ya samar da fitattun ’yan siyasa, amma bai samu irin wannan tallafi wajen samar da masallacin dindindin ba.

Kara karanta wannan

Tana sama tana dabo kan shirin kirkirar wasu jihohi, Gwamna ya hango matsala

Ya roki gwamnan da ya ƙara kammala aikin ta hanyar gina masallaci da makarantar Islamiyya domin yara a yankin.

Ya ce a halin yanzu, mazauna yankin suna gudanar da ibada ne a wani ƙaramin gini na wucin gadi kusa da hanya.

Tukur-Kola ya bayyana cewa ginin bai wadatar da bukatun al’ummar yankin ba, saboda ƙarancinsa da kuma yawan masu ibada.

Ya ƙara da cewa wurin yana da tazarar wasu ’yan mita daga gidan dangin Malami, tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma ministan shari’a.

Malami ya riƙe wannan mukami daga shekarar 2015 zuwa 2023, amma Tukur-Kola ya ce bai tallafa wajen sayen ko gina masallacin ba.

Shi ma limamin masallacin, Mallam Muhammad Sani, ya nuna godiyarsa ga gwamnan Kebbi saboda wannan tallafi da ya samar wa al’umma.

Sani ya yi addu’ar Allah ya taimaki Idris wajen cimma burinsa na siyasa, tare da ci gaba da shiryar da shi kan al’amuran jihar.

Gwamna ya yi Allah wadai da harin yan bindiga

Mun ba ku labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Lafagu, inda suka kashe basaraken ƙauyen tare da tilasta wa mazauna gudun hijira zuwa wuraren da suka fi aminci.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Ondo bayan mummunan hatsarin jirgin sama da ya kashe mutane

Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya yi Allah-wadai da kisan basaraken, yana mai bayyana harin a matsayin dabbanci.

Gwamnatin jihar Kebbin ta tabbatar da cewa tana aiki da jami’an tsaro domin kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.