Jerin Laifuffukan da Hukumar EFCC Ke Bincikar Godwin Emefiele a Kansu

Jerin Laifuffukan da Hukumar EFCC Ke Bincikar Godwin Emefiele a Kansu

  • Hukumar hana cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta fara bincikar Godwin Emefiele
  • Hukumar EFCC ta fara gudanar da bincike kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) bayan ta cafke shi
  • Akwai manyan laifuffuka da hukumar ke bincikar Emefiele a kansu ciki har da ciyo bashin dala biliyan 15 da daga ƙasashen ƙetare

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a ranar Juma'a, 27 ta fara gudanar da cikakken bincike kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Babban abin da hukumar ke bincikar Emefiele a kansa shi ne bashin dala biliyan 15 da aka ciyo daga ƙasashen ƙetare, rahoton TheNation ya tabbatar.

EFCC ta fara tuhumar Emefiele
Laifuffukan da hukumar EFCC Ke tuhumar Godwin Emefiele a kansu Hoto: Pius Utomi, Kola Sulaimon.
Asali: Getty Images

Emefiele zai kuma yi bayanin yadda babban bankin ya kashe Naira biliyan 74.84 wajen samarwa da fitar da kuɗaɗe ciki har da sabbin takardun kuɗi na Naira.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

Zarge-zargen dai ƙari ne kan zargin zamba wanda jami’in bincike na musamman, Jim Obazee, wanda ke duba ayyukan CBN ya bankaɗo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obazee, wanda kwamitinsa ke haɗa kai da hukumar binciken ƴan sandan Najeriya, ya kuma miƙa rahoton wucin gadi kan CBN ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Waɗanne zarge-zarge ne EFCC ke bincikar Emefiele?

An tabbatar da cewa, kwamitin jami'an EFCC ya fara bincikar Emefiele kan zarge-zargen da ake masa, waɗanda suka haɗa da:

  • Zargin basussukan ƙasashen ƙetare na dala biliyan 15
  • Kashe N74.84bn kan sauya fasalin Naira, samarwa da raba kuɗaɗe
  • Zargin zamba a shirin Anchor Borrowers Scheme
  • Binciken kuɗi kan CBN mai cike da dambarwa
  • Samun lasisin banki, Fintech da wasu manyan jami'an CBN suka yi
  • Bayar da kwangilolin biliyoyin Naira mai cike da zargi

Wani majiya daga EFCC ta ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wasu Hatsabiban 'Yan Fashi Biyu Suka Tsere Daga Gidan Yari a Jihar Arewa

“Emefiele yana hannunmu kuma tuni ya ke amsa tambayoyi kan wasu batutuwa ko zarge-zargen da ake yi masa daga wata tawagar da ke ƙarƙashin kulawar daraktan ayyuka, Abdulkarim Chukkol."
"A matsayinmu na hukuma, ba za mu yi magana a kan lamarinsa ba domin kada mu kawo cikas ga binciken da ake yi."

Emefiele Ya Yi Murabus

A baya rahoto ya zo cewa Godwin Emefiele ya yi murabus daga shugabancin babban bankin Najeriya (CBN).

Emefiele ya yi murabus ne bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa bisa wasu zarge-zarge da ake yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel