Gwamnatin Neja ta kara kudin jami'ar IBB daga N52,500 zuwa sama da N200,000

Gwamnatin Neja ta kara kudin jami'ar IBB daga N52,500 zuwa sama da N200,000

  • Bayan na Kaduna, jami'ar jihar Neja ta kara kudin makaranta
  • Dalibai sun nuna bacin ransu kan wannan sabon mataki
  • Wannan ya biyo bayan barazanar da ASUU take yi na sake komawa yajin aiki

Lapai, Niger - Hankalin dalibai ya tashi a jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai IBBUL, sakamakon karin kudin makarantar da hukumomin jami'ar suka yi.

A ranar Talata, shugabannin jami'ar sun sanar da dalibai cewa an kara kudin makarantar ga dukkan dalibai.

A cewar takardar sanarwar da Legit Hausa ta samu ranar Alhamis wacce Rijistran jami'ar, M.A Abdullahi ya rattafa hannu, dalibai zasu fara biyan kudi har N200,000.

A karin da aka yi, sabbin dalibai yan asalin jihar Neja zasu fara biyan N129,675.00 yayinda tsaffin dalibai zasu fara biyan N67,925.00.

Dalibai kuma wadanda ba yan asalin jihar ba zasu fara biyan N200,210.00 yayinda tsaffin zasu fara biyan N117,325.00

Gwamnatin Neja ta kara kudin jami'ar IBB daga N52,500 zuwa sama da N200,000
Gwamnatin Neja ta kara kudin jami'ar IBB daga N52,500 zuwa sama da N200,000
Asali: Original

Wani sashen sanarwan yace:

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP

"Muna sanar ga daukacin jama'a, musamman iyaye, sabbi da tsaffin daliban jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai, cewa shugabannin makarantar a zamansu na 50 ranar Talata, 1 ga Yuni, 2021, sun amince da kara kudin dukkan dalibai daga sabuwar kakar 2020/2021."
"Saboda haka, dukkan sabbi da tsaffin dalibai su fara rijista ranar 16 ga Agusta, 2021. Duk wanda kuma bai yi da wuri ba za'a ci shi tara."

Kungiyar ASUU na barazanar shiga sabon yajin aiki, sun bayyana dalili

A bangare guda, Malaman jami'o'in gwamnati a duk fadin kasar suna barazanar shiga wani sabon yajin aiki.

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi wannan barazanar a lokacin da ta zargi Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da kin biyan albashi da kuma fitar da kudaden alawus na sama da ma’aikata 1000 na tsawon watanni 13.

Lazarus Maigoro, shugaban ASUU na jami’ar Jos, ya yi wannan barazanar a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Fitacciyar jigon jam'iyyar APC ta sauya sheka, ta koma PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel