Ministan Buhari Ya Yi Magana da Abba Kabir Ya 'Sake' Matarsa a bainar Jama'a
- Tsohon minista Solomon Dalung ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yadda ya bayyana batun rabuwa da matarsa
- Tsohon ministan ya ce babu laifi gwamnan ya raba aure, amma bai kamata ya yi amfani da kalaman da za su rage mutuncin matar tasa ba
- Dalung ya gargadi Abba cewa siyasa da sauyin kawance za su iya gushewa, amma 'ya'yansa za su ci gaba da tunawa da lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya yi magana kan batun rabuwar auren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da matarsa, inda ya soki yadda gwamnan ya bayyana matakin da ya dauka.
Dalung ya ce ba ya adawa da shawarar Abba ta kawo karshen aurensa idan hakan ne yake so da gaske, amma ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka gudanar da lamarin.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa

Source: Facebook
A cikin wani bayani da ya wallafa a Facebook, tsohon ministan ya ce babu wanda ya kamata a tilasta masa ci gaba da zaman aure idan dangantakar ta lalace.
Sai dai ya bayyana cewa abin da ya dame shi shi ne kalaman da ake dangantawa da gwamnan na cewa ya amince da sakin matar tasa domin ya samu damar "cike gurbin da ya rage".
Dalung ya kare mutuncin matar Abba
Tsohon ministan ya ce bai dace mutum ya dauki batun rabuwa da matar da suka shafe kusan shekaru 20 tare da ita, suka haifi 'ya'ya shida, kamar wani mukami da aka bari babu mai rike da shi ba.
Ya jaddada cewa ko da menene ya faru a tsakanin gwamnan da matarsa, hakan bai kamata ya hana shi mutunta matar ba, musamman ganin cewa ita ce mahaifiyar 'ya'yansa.
Dalung ya kuma yi nuni da cewa rashin jituwar siyasa da ka iya kasancewa tsakanin Abba da surukinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, bai kamata ta shafi yadda gwamnan yake mu'amala da matarsa ba.

Source: Facebook
Abba zai ji dadi matarsa ta yi masa haka a fili?
Solomon Dalung ya yi tambayar ko da Abba Kabir zai amince idan matarsa ta fito kafar yada labarai ta bayyana korafe-korafen da take da su game da yadda aka gudanar da aurensu.
Ya ce idan matar gwamnan ta fito ta bayyana abubuwan da ta fuskanta a zaman aurensu, shin Abba zai ga hakan a matsayin matakin da ya dace?
A cewarsa, akwai bambanci tsakanin mutum ya yi amfani da hakkinsa na sakin aure da kuma fito wa fili ya yi abin da zai iya bata sunan wadda yake son rabuwa da ita.
Ya bayyana cewa sakin aure zabin mutum ne, amma yadda aka gudanar da shi a bainar jama'a na iya nuna rashin taka-tsantsan da la'akari da jin dadin wani.
Dalung ya tunatar da muhimmancin mutunta iyalai
Tsohon ministan ya ce Abba Kabir Yusuf gwamnan Kano ne, kuma duk da cewa siyasa na iya sauyawa, kawance na iya wargajewa, dangantakarsa da Kwankwaso ma na iya lalacewa, akwai abin da ba zai gushe ba.
Ya ce 'ya'yan gwamnan za su ci gaba da tunawa da yadda aka tafiyar da matsalar iyalinsu, ko da kuwa siyasar da ake yi a yanzu ta canza.
Dalung ya bayyana cewa shugabanci ba wai ikon yanke hukunci kawai ba ne, har da sanin lokacin da ya kamata mutum ya yi shiru maimakon kokarin samun nasara a muhawara.
Ya kara da cewa ba dole sai mutum ya ci gaba da zama da mace a matsayin mata ba kafin ya mutunta ta, sannan bai kamata a wulakanta mahaifiyar 'ya'yansa domin tabbatar da cewa aure ya mutu ba.
Matar Abba Kabir ya nemi saki
An ji cewa Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamna Abba Yusuf ta biyu, ta shigar da ƙarar neman kashe aurensu a wata kotun Shari’a da ke Abuja.
Takardar sammaci ta umarci gwamnan da ya gurfana a gaban kotun ranar 17 ga Nuwamba, 2026.
Zainab ta ce soyayya da kusancin da ke tsakaninsu sun lalace, inda ta bayyana shirinta na biyan Gwamna Abba sadakin da ya biya lokacin aurensu.
Asali: Legit.ng

