Gwamnati Ta Tabbatar da Kananan Yara 17, 000 Sun Kamu da Wata Cuta a Jihar Kano

Gwamnati Ta Tabbatar da Kananan Yara 17, 000 Sun Kamu da Wata Cuta a Jihar Kano

  • Kwamishinan Lafiya na Kano, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya ce an gano yara sama da 17,000 na ɗauke da cutar lamoniya a jihar
  • Dr. Abubakar ya bayyana cewa yara sama da 300,000 a faɗin Najeriya sun kamu da cutar a bana
  • gwamnatin jihar Kano ta horas da ma’aikatan lafiya kan dabaru na musamman na kula da cututtukan yara, domin inganta ingancin kulawar da ake ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Akalla yara 17,000 a Jihar Kano aka gano suna ɗauke da cutar lamoniya, kamar yadda Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana.

Wannan adadi na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, Nabilusi Abubakar K/Na’isa, ya fitar yau Jumu'a.

Abba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin da yake jagorantar taro a fadar gwamnatin jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Yara 17,000 sun kamu da lamoniya

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ba ya son a fitar da takardun Tinubu, ya shigar da bukata gaban kotu

Punch ta rahoto cewa sanarwar ta ce kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin bikin tunawa da Ranar Cutar Lamoniya ta Duniya da kuma Ranar Ciwon Sukari ta Duniya a Kano.

“An gano yara sama da 17,000 a Jihar Kano suna ɗauke da cutar lamoniya,” in ji Abubakar Yusuf.

An ce an shirya taron ne domin wayar da kan jama’a game da cutar da ke kama yara, da kuma ƙarfafa hanyoyin kariya, gano cutar da wuri da kuma ba da ingantaccen magani, domin rage mace-macen yara sakamakon cutar.

Yara 300,000 sun kamu a Najeriya

Dr. Abubakar Yusuf ya kuma bayyana cewa yara sama da 300,000 a faɗin Najeriya sun kamu da cutar lamoniya a bana.

“Yara sama da 300,000 a faɗin Najeriya sun kamu da cutar lamoniya a bana,” in ji shi.

Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa cutar na iya zama barazana ga rayuwa, musamman ga ƙananan yara. Ya ƙara da cewa rashin isasshen abinci mai gina jiki na ƙara haɗarin kamuwa da cutar da kuma tsananta yanayinta.

Ya ce gwamnatin jihar Kano ta horas da ma’aikatan lafiya kan dabaru na musamman na kula da cututtukan yara, domin inganta ingancin kulawar da ake ba su.

Kara karanta wannan

Barayi sun shiga masallaci sun sace fankoki sama da 20 a Kano

Mutane miliyan 500 na da ciwon sukari

Dangane da cutar sukari, Dr. Yusuf ya bayyana cewa cutar na daga cikin manyan ƙalubalen lafiya da ke buƙatar kulawa ta musamman domin kauce wa matsalolin da ka iya biyo bayanta.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce sama da mutane miliyan 500 a faɗin duniya na rayuwa da cutar sukari, yayin da aka kiyasta cewa kashi 7.5% na mazauna Jihar Kano su ma na fama da ita.

“Sama da mutane miliyan 500 a duniya na rayuwa da cutar sukari, yayin da aka kiyasta cewa kashi 7.5% na mazauna Jihar Kano su ma ke fama da cutar,” in ji Yusuf.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Kano ta ƙara ƙaimi wajen tallafa wa masu fama da cutar ta hanyar inganta ayyukan kiwon lafiya da samar da kayan aikin jinya.

Bakuwar cuta ta barke a Zamfara

Kun ji cewa ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta ce an samu mutum 38 da suka kamu da wata bakuwar cuta da ba a gano asalinta ba.

An fi samun masu fama da cutar a ƙaramar hukumar Shinkafi, yayin da aka kuma samu wasu a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262