Abin Tausayi: Yan Bindiga Sun Rutsa 'Yan Gudun Hijira a Hanyar zuwa Gona
- Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace ’yan gudun hijira shida a yankin Kaso da ke ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna
- Bayanai sun nuna cewa an sace mutanen ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu, inda daga baya aka saki biyu saboda halin lafiyarsu
- Mai kula da ’yan gudun hijira ya ce mace na cikin waɗanda aka sace, yayin da ’yan sanda ba su kai ga magana kan lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da ’yan gudun hijira shida a Anguwan Baijuwa, Kaso, da ke ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da yan gudun hijiran ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu.

Source: Original
An sace yan gudun hijira a Kaduna
Sakataren magajin garin ƙauyen Kaso, Jonah Baba, ya tabbatar wa jaridar Leadership da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun tare hanya a kusa da rafin Romi, a yankin ƙauyen Suleja da ke Kaso.
Ya ce waɗanda aka sace manoma ne da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Mararaban Uden.
Jonah Baba ya ce:
“Sun yi garkuwa da mutane shida, amma yanzu sun saki mutum biyu daga cikinsu."
An tabbatar da sako mutane 2
Mai kula da ’yan gudun hijira na Maraban Rido, Sule Adams, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace mutanen ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026.
Adams ya bayyana cewa dukkan waɗanda aka sace ’yan gudun hijira ne da suka bar wuraren da suke fakewa domin zuwa gonakinsu, kafin maharan su kai musu hari kuma su tafi da su.

Kara karanta wannan
Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta
Ya ce daga baya waɗanda suka yi garkuwa da su sun saki mutum biyu saboda yanayin lafiyarsu, yayin da sauran huɗu ke ci gaba da kasancewa a hannunsu.
Adams ya ƙara da cewa akwai mace a cikin waɗanda aka sace, kuma har yanzu ba su ji komai daga masu garkuwan ba.
Ya nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ’yan gudun hijira ke fuskanta, musamman ganin cewa da dama daga cikinsu sun dogara ne da noma domin ciyar da iyalansu da kuma samun abin gudanar da rayuwa.
Lamarin ya ƙara jefa fargaba kan tsaron ’yan gudun hijira a yankin, musamman waɗanda ke ƙoƙarin komawa gonakinsu duk da barazanar rashin tsaro.
A halin yanzu, rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ba ta ce komai kan sabon lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Mutum 17 sun mutu a hannun yan bindiga
Kun ji cewa kungiyar CSW ta bayyana cewa akalla masu ibada 17 da aka sace yayin harin coci-coci uku a Ariko, Kaduna, sun mutus hannun yan bindiga.
An saki wasu mutane takwas bayan shafe watanni biyar a hannun masu garkuwa da su, yayin da wasu 12 suka tsere a lokuta daban-daban in ji kungiyar.
Asali: Legit.ng
