Gwamna zai Yi Rabon Tsabar Kudi har Naira Biliyan 6 ga Talakawa

Gwamna zai Yi Rabon Tsabar Kudi har Naira Biliyan 6 ga Talakawa

  • Gwamnatin jihar Ogun ta fara rabon N6bn ga kungiyoyin mata 3,855 da ke kananan hukumomi hudu domin bunkasa sana’o’insu
  • Shirin na karkashin hadin gwiwar gwamnatin tarayya da Bankin Duniya ne, kuma an tsara shi ne domin kara karfin harkokin kasuwancin da mata ke jagoranta
  • Gwamna Dapo Abiodun ya ce kudin ba tallafi ne na kyauta ba, sai dai wani tsarin samar da jari da zai taimaka wajen kafawa da fadada sana’o’i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun – Gwamnatin jihar Ogun, tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da Bankin Duniya, ta fara rabon N6bn ga kungiyoyin mata 3,855.

An kaddamar da rabon kudin ne a Ijebu-Ode, inda aka bayyana cewa shirin na da nufin bunkasa kasuwancin mata, karfafa tattalin arzikin gidaje da kara shigar mata cikin harkokin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

Gwamna Dapo Abiodun
Wajen raba tallafi a jihar Ogun. Hoto: Ogun State Government
Source: Facebook

Abin da shirin zai yi wa mata

Punch ta wallafa cewa Gwamna Dapo Abiodun, wanda tsohuwar Kwamishiniyar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma, Motunrayo Adeleye, ta wakilta, ya ce an tsara kudin ne domin taimaka wa mata su sauya daga kananan sana’o’i zuwa kasuwanci mai dorewa.

Ya ce kungiyoyin da suka amfana sun cika sharudan shirin, ciki har da halartar taruka akai-akai, tara kudi, bayar da rance a cikin kungiyoyi, bude asusun banki da kuma shirya tsare-tsaren zuba jari.

Abiodun ya bayyana cewa matan sun tara N2.6bn a cikin wata bakwai da suka gabata, yayin da rancen da suka samu ta kungiyoyin ya haura N4bn.

Ya ce alkaluman na nuna yadda kungiyoyin mata suka samu kwarewar sarrafa kudi, amana, jajircewa da daukar nauyin juna.

Yadda za a raba kudin

Abiodun ya bayyana cewa N6bn din ba tallafi ne na kyauta ba, illa tsarin samar da jari da aka tsara domin taimaka wa mata su kafa ko fadada sana’o’i, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar iyalansu.

Kara karanta wannan

Sultan ya kausasa harshe kan zubar da jini, ya yi kira ga Tinubu

Ya ce shirin ya samo asali ne daga Nigeria for Women Project da aka fara a jihar Ogun a watan Disamba 2020, bayan da Bankin Duniya da gwamnatin tarayya suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin a 2018.

Gwamnan ya ce shirin farko ya samar da kungiyoyin mata 3,792 a cikin al’ummomi 1,003 da ke kananan hukumomin Odeda, Ikenne, Ijebu North-East da Yewa North.

A sakon da ya wallafa a X, Ya kara da cewa an horar da masu taimakawa kungiyoyin mata 368 tare da tura su aiki, yayin da mata 67,094 suka samu tallafin kai tsaye a watan Afrilu 2022.

Mata 124,062 sun amfana

Gwamnan ya ce sabon bangaren shirin ya fadada zuwa kananan hukumomi bakwai, wato Ifo, Ado-Odo/Ota, Ijebu-Ode, Sagamu, Abeokuta North, Ipokia da Remo North.

Ya ce zuwa ranar 21 ga Satumba 2026, an kafa kungiyoyin mata 5,394 karkashin shirin Scale-Up, inda suka kai ga mata 124,062.

Abiodun ya ce shirin ya kuma mamaye al’ummomi 3,489, tare da horar da masu taimakawa kungiyoyin mata 664.

Taswirar jihar Ogun
Taswirar jihar Ogun a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya ce kimanin jihohi 26 sun ziyarci Ogun domin koyon tsarin shirin, yayin da Bankin Duniya ya amince da jihar a matsayin cibiyar horaswa.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya ruguzo kasa bayan Trump da Iran sun fahimci juna

Magana kan kudin tallafin mai

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya ce gwamnonin jihohi ne ya kamata su yi bayani kan yadda ake amfani da kudaden da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, ba Shugaban Kasa Bola Tinubu ba.

Rahoto ya nuna cewa Abiodun ya bayyana hakan ne a wani gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.

Gwamnan ya ce karin kudin da jihohi ke samu bayan cire tallafin man fetur ya sanya gwamnonin jihohi suka fi dacewa su yi bayanin yadda ake amfani da kudin wajen ayyukan raya kasa da shirye-shiryen tallafa wa jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng