Hukumar Fansho(Pencom)
Gwamnatin Kano ta biya N21bn daga cikin Naira biliyan 48.6 da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta hana wasu daga cikin 'yan fansho da suka hidimtawa jihar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tuna da ma'aikatan da suka yi ritaya da wadanda suka rasu. Gwamnan ya umarci a fitar da kudade domin biyansu hakkokinsu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fara biyan karin kudaden fansho ga ma'aikatan da suka yi ritaya.
Gwamna Abba Yusuf ya saki N5bn ga masu fansho, ya kuma sanar da karin mafi karancin fansho zuwa N20,000. Abba ya ce Ganduje ya jefa 'yan fansho a cikin wahala.
Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta na tabbatar da biyan dukkanin 'yan fansho hakkokinsu kamar yadda ta yi alkawari kafin a zabe ta a shekarar 2023.
Kungiyar ƴan fansho ta jihar Taraba ta bayyana cewa Gwamna Agbu Kefas zai inganta walwalarsu idan ya koma zango na biyu, ta ce ƴaƴanta suna tare da shi.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kori shugabar hukumar fansho ta ƙasa watau PTAD watanni 13 bayan sabunta naɗinta, ya maye gurbin da mace.
Wasu gungun ƴan fansho sun fita zanga zanga a ma'aikatar kudi ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, sun nemi gwsmnati ta biyasu hskkokinsu na tsohon tsarin fansho.
Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi ya kafa tarihi bayan shekaru 20, ya amince da karin alawus na N10,000 ga dukkan masu kataɓar fansho a jihar.
Hukumar Fansho(Pencom)
Samu kari