EFCC Ta Maida Makarantun da Ta Karbe hannun 'Barayi’ Sun Zama Jami'o'in Gwamnati

EFCC Ta Maida Makarantun da Ta Karbe hannun 'Barayi’ Sun Zama Jami'o'in Gwamnati

  • Jami'ar NOK da aka ƙwace a Kudancin jihar Kaduna yanzu ta zama jami'ar tarayya mai ɗalibai kusan 2,000
  • Hukumar EFCC ta kuma ƙwace wata babbar jami'a mai zaman kanta a jihar Kebbi, an mika wa gwamnati
  • Maganganun Ola Olukoyede sun nuna jami’ar Rayhan ta zama makarantar da ke karkashin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya ce wata jami’a da suka kwato a kotu ta zama ta gwamnatin tarayya.

EFCC ta yi nasara a wata shari’a da aka yi game da yadda aka bi aka mallaki wannan makaranta, kuma kotu ta ba ta gaskiya.

EFCC.
Wani daga cikin gine-ginen da EFCC ta karbe Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Jami'ar kudi ta zama ta Gwamnatin tarayya

A ranar Juma’a jaridar Punch ta rahoto cewa yanzu wannan jami’a mai dalibai 1, 909 ta zama mallakin gwamnatin tarayya.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a jiya, an ce Ola Olukoyede ya nuna tsohuwar jami’ar NOK da ta zama ta gwamnati.

Kara karanta wannan

Bayan ƙalubalantar shi kan gina jami'a a Arewa, Atiku ya ce ba domin riba ya yi ba

Jami’ar NOK da ke Kachia a jihar Kaduna ta zama cikin jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya Kachia (FUASK) da aka kafa a 2025.

Makarantar da aka karbe saboda mallakarta ta hanyar sata yanzu jami’ar tarayya ce.

Makarantar da ke jihar Kaduna ta zama Jami’ar kimiyya ta tarayya kuma a Disamban 2025, an dauki dalibai 1, 909 a nan.

Mista Ola Olukoyede ya ce ba don an karbe wannan gini ba, da daliban ba za su taba shiga dakin taro irin na makarantar ba.

Kafin hakan ta faru, ana ganin dama makarantar za ta bunkasa tattalin arzikin yankin da aka gina ta a Kudancin jihar Kaduna.

Jami'ar da EFCC ta karbe a jihar Kebbi

Olukoyede ya kuma ce akwai wata babbar jami’ar kudi da kotu ta damka wa gwamnatin tarayya da aka yi kara a kotu.

"Kuna bukatar ku je wannan jami’a a Kebbi. Tana da bangaren wucin gadi da kuma na din-din-din."

- Shugaban EFCC

Shugaban EFCC ya ce gidan da aka gina wa shugaban jami’ar kawai ya fi girman inda shugaban kasa yake ciki a fadar Aso Rock.

Kara karanta wannan

Daliban ABU Zaria sun kera na'urar da makafi za su rika tafiya da ita cikin salama

A maganar da ya yi, Olukoyede bai ambaci sunan makarantar ba, amma babu mamaki jami’ar Rayhan ce da aka yi ta shari’a kan ta.

Jami'ar Rayhan
Jami'ar Rayhan da kotu ta mallaka wa gwamnati a Kebbi Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Abubukar Malami wanda ya yi ministan shari’a a gwamnatin Muhammadu Buhari ya gina jami’ar da kotu ta kwace a watan Yulin 2025.

Ban da gine-gine, jami’ar hukumar EFCC sun karbo kudi da ake zargin na haramun ne.

ICPC ta kori jami'i saboda El-Rufai

An ji Aichatou Assabe El-Rufai ta jawo ICPC ta kori jami'in tsaro sakamakon taimaka mata wajen ganin mijinta ba tare da bin ka'ida ba.

Hukumar ICPC ta sallami Daniel Stephen bayan na'urar CCTV ta kama shi yana shigar da matar tsohon gwamnan ta ga mijinta da ke tsare.

Stephen ya amsa laifin cewa ya taimaka mata wajen shiga dakin da aka tsare El-Rufai don yin magana a kan shari'arsu da ake yi a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng