Duhu zai Kare: Bankin Duniya zai Saka Kudi don Inganta Lantarkin Najeriya
- Bankin Duniya ya ce zai tallafa wa sauye-sauyen da Najeriya ke shirin yi kan tsarin harajin wutar lantarki da tallafin da gwamnati ke bayarwa
- Bankin ya ce matakan na daga cikin kokarin dawo da dorewar bangaren wutar lantarki da kuma inganta samar da wuta ga gidaje da ‘yan kasuwa
- Ya bayyana cewa shirye-shiryen da yake tallafawa za su taimaka wajen samar da wutar lantarki ga sama da ‘yan Najeriya miliyan 32 a yankuna daban daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Bankin Duniya ya ce zai tallafa wa sauye-sauyen tsarin harajin wutar lantarki da tallafin gwamnati a Najeriya domin samar da wadataccen kudi a bangaren wutar lantarki.
Bankin ya bayyana hakan ne a cikin tsarin hadin gwiwar kasashe na shekaru shida da ya tsara wa Tarayyar Najeriya daga kasafin kudin shekarar 2026 zuwa 2032.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da fama da matsalolin wutar lantarki a Najeriya, musamman a karkara.
Bankin Duniya zai tallafa
A cewar takardar, bankin duniya zai mayar da hankali wajen inganta samun wutar lantarki da tabbatar da ingancinta ga gidaje da ‘yan kasuwa ta hanyoyin layin wutar lantarki da kuma hanyoyin da ba su dogara da tushen wutar kasar ba.
Matakin na cikin tsarin cimma manufofin yarjejeniyar Mission 300 ta Najeriya, wadda ke da nufin kara yawan mutanen da ke samun wutar lantarki.
Bankin ya ce zai kuma tallafa wa sauye-sauyen da za su dawo da dorewar harkar kudi, musamman kan tsarin haraji da tallafin wutar lantarki, tsare-tsaren zuba jari masu gasa da kuma ingantaccen tsarin kula da bangaren wutar lantarki.
Najeriya na da gibin lantarki
Bankin Duniya ya bayyana cewa Najeriya ce ke da mafi girman gibin samun wutar lantarki a duniya, inda sama da mutane miliyan 86 ba su da damar samun wutar lantarki.
Ya ce yawan katsewar wuta ya tilasta wa gidaje da ‘yan kasuwa dogaro da janareto masu tsada, lamarin da ke rage yawan aiki da ci gaban kamfanoni.

Source: Facebook
Bankin ya kara da cewa halin da bangaren wutar lantarki ke ciki ta fuskar kudi bai dore ba, inda gibin kudin harajin wutar lantarkin da aka kiyasta ya kai dala biliyan 2.45 a karshen shekarar 2025.
Maganar takarar Tinubu a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APM, ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2027 kan abin da ta bayyana a matsayin zarge-zargen da ba a warware ba.
Jam'iyyar ta ce rahotannin kalubalantar Tinubu kan sakin wasu takardu da ake zargin FBI, da Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi, DEA, ke rike da su sun kara jawo hankalin jama'a kan lamarin.
APM ta ce tana da yakinin cewa kotunan Amurka za su yanke hukunci kan batun bisa doka da kuma hujjojin da ke gaban kotu, yayin da ta yi ikirarin cewa lauyoyin Tinubu sun nemi a hana sakin takardun.
Asali: Legit.ng

