Manyan Wayoyin Android 5 da Za Su Iya Gogayya da iPhone 18 a 2026
- iPhone 18 Pro na Apple yana farawa daga $1,199, lamarin da ya sanya masu saye cikin rukunin manyan wayoyi masu tsada tare da wasu wayoyin Android masu karfi
- Manyan wayoyin Android daga Samsung, Google, Xiaomi, OnePlus da Vivo suna fafatawa wajen kyamarori, tsawon lokacin da batir ke dauka da kuma basirar AI
- Kowane daya daga cikin wayoyin Android din yana da wasu fa’idodi na musamman kan iPhone 18 Pro, daga kyamarar 200MP zuwa batir mai karfin 6,510mAh
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Wayoyin iPhone 18 ta Apple sun zo da wasu muhimman abubuwa masu karfi, ciki har da ingantattun kyamarori, karin tsawon lokacin batir da kuma karin fasahohin basirar wucin gadi ta AI.
Da farashinsu ya kai $1,199 da $1,299 bi da bi, wayoyin biyu sun shiga kai tsaye cikin rukunin manyan wayoyi masu tsada.

Source: Getty Images
Rahoton Yen ya nuna cewa kamfanonin kera wayoyin Android ba su shirya tsaya a can baya ba ba tare da fafatawa da Apple ba, an fitar da manyan mayoyi da za su iya gogayya da iPhone 18.

Kara karanta wannan
Yayin da rikicin mashigar Hormuz ke kara tsananta, farashin mai ya tashi a Najeriya
1. Samsung Galaxy
Galaxy S26 Ultra na Samsung shi ne mafi kusancin abokin hamayya ga iPhone 18 Pro Max. Allon wayar mai girman inci 6.9, yana aiki da saurin sabunta hoto na 120Hz.
Yayin da wayar ke amfani da manhajar Snapdragon 8 Elite Gen, tare da zabukan da suka kai 16GB RAM da ajiyar bayanai 1TB.
Babbar kyamarar 200MP, kyamarar ultrawide 50MP da kuma kyamarar telephoto 50MP ne ke jagorantar tsarin daukar hoto, yayin da batir mai karfin 5,000mAh, caji mai waya na 60W ke dauke da wayar.
2. Google Pixel 11 Pro XL
Google Pixel 11 Pro XL ta tunkari wannan fafatawa ta wata hanya daban, inda ya fi mayar da hankali kan daukar hoto ta hanyar sarrafa bayanai da kuma basirar wucin gadi maimakon yawan karfin bayanan fasaha kawai.
Tensor G6 na wayar ne ke tafiyar da zurfin amfani da basirar wucin gadi a tsarin kyamara da kuma muhimman ayyukan wayar, tare da babbar kyamarar 50MP wadda aka hada da kyamarar ultrawide 48MP da kuma telephoto 48MP.

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Source: Getty Images
3. Xiaomi 17 Ultra
Masu sha’awar daukar hotuna suna iya sayen Xiaomi 17 Ultra, wadda ke dauke da tsarin kyamara mai alamar Leica, wanda ya dogara kan babbar kyamara 50MP mai girman inci daya da kuma kyamarar telephoto 200MP.
Batir mai karfin 6,000mAh da fasahar HyperCharge ta 90W sun ba ta gagarumin fifiko wajen saurin caji idan aka kwatanta da wasu abokan hamayyarta.
4. OnePlus 15
Rahotanni sun nuna cewa an tsara wayar OnePlus 15 ne musamman domin masu amfani da ke bukatar karfin aiki na tsawon lokaci.
Baya ga manhajar Snapdragon 8 Elite Gen 5, tana da allon LTPO mai saurin sabunta hoto na 165Hz, wanda ya fi ma’aunin 120Hz da ake samu a mafi yawan manyan wayoyin zamani.
An samar da ingantaccen tsarin sanyaya wayar domin taimakawa wajen ci gaba da samun karfin aiki yayin wasannin da ke bukatar kuzari mai yawa da kuma ayyukan da ke amfani da na’urorin wayar sosai.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Hare haren jirage marasa matuka sun jawo gagarumar matsala a Saudiyya
5. Vivo X300 Pro
Vivo X300 Pro ta kammala jerin wayoyin 5 da wani zabin da ya fi mayar da hankali kan daukar hotuna. Tsarin kyamararta ya kunshi babbar kyamara 50MP, kyamarar ultrawide 50MP da kuma kyamarar telephoto 200MP ZEISS APO.
Wayar tana amfani da manhajar Dimensity 9500 ta MediaTek tare da har zuwa 16GB RAM. Haka kuma tana da batir mai karfin 6,510mAh.
Za a ba dalibai data
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce daliban Najeriya za su rika samun data kyauta mai girman 100MB a kowace rana domin shiga wasu shafukan ilimi da manhajojin koyon karatu na zamani.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ce ta samar da shirin tare da hadin gwiwar kamfanonin sadarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da shirin samar da damar shiga shafukan ilimi da manhajojin koyon karatu kyauta ba tare da cire kudin data ba.
Asali: Legit.ng