Maryam Dan Azumi: Abin da Tinubu Ya Ce kan Yarinyar da Ta Lashe Gasar Kur'ani

Maryam Dan Azumi: Abin da Tinubu Ya Ce kan Yarinyar da Ta Lashe Gasar Kur'ani

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Dan’Azumi murnar lashe gasar Alƙur’ani ta King Abdulaziz karo na 46 a Saudiyya
  • Maryam ta doke mahalarta daga ƙasashe 132, inda ta lashe kyautar Riyal 300,000, kwatankwacin Naira miliyan 120
  • Tinubu ya ce nasarar Maryam ta jawo alfahari ga Najeriya, tare da yabawa iyayenta, malamai da masu ba ta horo bisa gudunmawarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Dan’Azumi, ‘yar Gombe murnar lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa.

Maryam ta zama zakara a rukunin mata na gasar Alƙur’ani ta King Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Masarautar Saudiyya.

Tinubu ya taya Maryam dan'azumi murna
Maryam Dan'azumi da ta lashe gasar Kur'ani a Saudiyya. Hoto: Yusuf Muhammad Dukku.
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a shafin X a yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Abin da zaɓaɓben gwamnan Osun ya fadawa Tinubu gaba da gaba a fadar shugaban kasa

Shugaba Tinubu ya yaba da bajintar Maryam da ƙwarewarta wajen karatun Alƙur’ani a gasar da aka gudanar a birnin Makka mai tsarki.

Maryam ta doke sauran mahalarta gasar daga ƙasashe 132, inda ta samu kyautar Riyal 300,000 na Saudiyya, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 120.

Shugaban ya ce nasarar Maryam ba nasara ce ta kashin kanta kawai ba, domin ta kuma zama abin alfahari ga Najeriya a duniya.

Tinubu ya bayyana cewa Maryam ta wakilci Najeriya yadda ya kamata, ta hanyar nuna ƙwarewa da zurfin ilimi wajen karatun Alƙur’ani mai girma.

Shugaban ya bayyana Maryam da yayarta, Hajara Ibrahim Dan Azumi, wacce ta lashe irin wannan gasa a Jordan a 2024, matsayin abin koyi.

Ya ce nasarar ‘yan’uwan biyu za ta iya zaburar da matasan Najeriya wajen neman ilimi, dagewa da kuma cimma manyan nasarori a rayuwa.

Tinubu ya taya Maryam dan'azumi murnar lashe gasar Kur'ani
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya yaba wa iyayen Maryam da Hajara, malamansu, masu ba su horo da duk waɗanda suka taimaka wajen haɓaka ƙwarewarsu.

Ya ce irin wannan nasara na bukatar sadaukarwa, jajircewa da kulawa mai yawa kafin mutum ya kai wannan matsayi na ƙwarewar Alƙur’ani.

Kara karanta wannan

'Yar jihar Gombe ta yi zarra a duniya, Maryam ta lashe gasar Kur'ani a Saudi

Shugaban ya kuma yaba wa hukumomin Saudiyya da masu shirya gasar saboda samar da wani babban dandali na duniya ga masu haddar Alƙur’ani.

Ya ce gasar tana ƙarfafa ƙwarewa wajen haddar Alƙur’ani, karatunsa, Tajwid, fahimtarsa da kuma zurfafa ilimi kan ma’anoni da tafsirinsa.

Tinubu ya sake tabbatar da aniyarsa ta tallafa wa shirye-shiryen da ke bunƙasa ilimin matasa, tarbiyyarsu da ci gabansu na addini.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da damar da za ta bai wa matasan Najeriya damar yin fice a cikin gida da ƙasashen waje.

Ya ce:

“Maryam Ibrahim Dan Azumi ta jawo wa Najeriya abin alfahari, nasararta a Makka ta nuna abin da matasanmu za su iya cimma muradudu.
“Lokacin da baiwa ta haɗu da ladabi, imani, aiki tuƙuru da horo mai kyau, matasa za su iya cimma manyan nasarori a duniya."

Shugaban ya yi wa Maryam fatan ci gaba da samun nasara yayin da take zurfafa karatunta na Alƙur’ani da sauran harkokinta na gaba.

Pantami ya taya Maryam dan'azumi muran

An ji cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taya Malama Maryam Ibrahim Dan'azumi murnar lashe gasar Al-Qur'ani ta duniya da aka gudanar a Makkah.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Maryam ta yi fice ne a bangaren mata na haddar izu 60 da tafsiri, inda ta lashe kyautar Riyal 300,000, kwatankwacin kusan Naira miliyan 120.

Pantami ya kuma bayyana farin cikinsa ganin cewa 'yar'uwar Maryam, Hajara Ibrahim Dan'azumi, ita ma ta taba lashe wata gasar Al-Qur'ani ta duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.