Uba Sani Ya Dauko Hanyar Gyara, Ya Nada Kwamishinoni 3, Hadimai 45

Uba Sani Ya Dauko Hanyar Gyara, Ya Nada Kwamishinoni 3, Hadimai 45

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya nada kwamishinoni a jihar domin bunkasa ayyukan gwamnati ana shirin zabe
  • Ben Kure, Daraktan Gudanarwa na hukumar yada labarai ta Kaduna, KSMC, na cikin wadanda aka nada
  • Ya bukaci wadanda aka nada su kawo sababbin dabaru tare da tabbatar da cewa ayyukansu sun yi daidai da manufofin gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya nada sababbin kwamishinoni uku, masu taimaka masa 45 da mambobin hukumomi 40.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa gwamnan ya yi hakan ne domin kara bunkasa ayyukan gwamnatinsa.

Uba Sani ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa
Gwamna Uba Sani na Kaduna yayin taro a jihar. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar, gwamnan ya ce nadin zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen sauyi, cewar Punch.

Abin da ake tsammani daga wadanda aka nada

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ji dadin kokarin Uba Sani, ya fadi wahalar da sarakuna ke ciki

Ya ce wadanda aka nada za su taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da kuma samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a Kaduna.

Sanarwar ta bayyana cewa Ben Kure, Daraktan Gudanarwa na hukumar yada labarai ta jihar Kaduna zai zama kwamishinan raya wasanni.

Gwamnan ya kuma nada Amina Akilu Dalhat a matsayin Kwamishiniyar Ayyuka na Musamman ta Farko, yayin da Abdullahi Garba Abbas zai rike matsayi na biyu.

A cewar Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Dokta Haliru Soba, wanda shi ne Babban Sakataren dindindin a Ma’aikatar Ilimi, zai zama Mataimakin Shugaban Ma’aikata mai kula da harkokin gudanarwa.

Gwamna Uba Sani ya kuma nada shugabanni da mambobin wasu muhimman hukumomi, ciki har da Alhaji Munir Jafaru, wanda zai zama shugaban hukumar kula da kiwon lafiya ta Kaduna.

Uba Sani ya nada kwamishinoni 3 da hadimai 45
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a yayin taro. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: Twitter

Wadanda aka nada mukamai a Kaduna

An kuma nada AVM Bashir Gamagira Saidu a matsayin shugaban hukumar ke da alhakin ayyukan sa ido da tsaro a al’umma, cewar Vanguard.

Sauran shugabannin sun hada da Mai Shari’a Gideon Isa Kurada, mai ritaya, wanda zai jagoranci Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya, da Esther Bago, shugabar Cibiyar koyar da sana'o'i da ci gaban al'umma.

Kara karanta wannan

'Abin da tsofaffin shugabanni ke tsoro Tinubu ya aiwatar saboda tausayin 'yan kasa'

Sanarwar ta ce gwamnan ya taya wadanda aka nada murna, yana mai cewa an zabe su ne bisa kwarewa, gaskiya da kuma jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka.

Gwamnan ya bukace su da su kawo sabbin dabaru, su guji sakaci sannan su daidaita ayyukansu da manufar samar da Kaduna mai sauyi da juriya.

Ya kuma yi musu fatan samun shiriyar Allah da nasara yayin da suke fara gudanar da sabbin ayyukan da aka dora musu domin tabbatar da gaskiya.

Uba Sani zai kara albashin sarakunan gargajiya

A baya, an ji cewa Gwamna Uba Sani na Kaduna ya amince da ƙarin albashi da alawus-alawus ga sarakunan gargajiya domin inganta jin daɗinsu.

Gwamnan ya kuma amince da biyan alawus ɗin tsaro kowane wata ga masarautu da masarautun ƙabilu 35, wanda ya fara aiki tun Satumba.

Gwamnatin Kaduna ta ce matakin zai ƙarfafa tattara bayanan sirri daga al’umma, tare da taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da laifuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.