Najeriya Ta Kara Samun Kudin Shiga, Tinubu Ya Bukaci Kara Kasafi daga N49.7trn
- Bola Tinubu ya bukaci a kara kasafin kudin 2025 daga N49.7trn zuwa N54.2trn, bisa karin kudin shiga da gwamnati ta samu daga wasu hukumomi
- Wasikar Shugaban kasa zuwa Majalisar Dattawa ta ce FIRS ta samu N1.4trn, Kwastam ta samu N1.2trn kuma sauran hukumomi sun tara N1.8trn
- Bayan karanta wasikar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya tura bukatar ga Kwamitin Kasafin Kudi don nazari kafin karshen Fabrairu
- Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya gabatar da kasafin kudi har N49.7trn a watan Disambar 2024 a gaban Majalisar tarayyar kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Majalisar Dokoki ta duba yiwuwar kara kasafin kudin shekarar 2025 da muke ciki.
Tinubu ya bukaci majalisar ta amince da kara kasafin daga N49.7trn zuwa N54.2trn saboda kara samun kudin shiga da aka yi.

Asali: Twitter
Kasafin kudi: Tinubu ya nemi bukata daga majalisa
Jaridar Tribune ta ce hakan na kunshe a wasikar Shugaban kasa zuwa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya karanto wasikar a zaman Majalisar a ranar Laraba 5 ga watan Janairun 2025 a birnin Tarayya Abuja.
A baya, Shugaban kasa ya gabatar da kasafin N49.7trn a gaban Majalisar wakilai da na dattawa a ranar 18 ga Disamba, 2024.
A cewar wasikar, karin ya biyo bayan samun N1.4trn daga hukumar FIRS da kuma N1.2trn daga Hukumar Kwastam.
Gwamnatin Tinubu ta samu karin kudi
Har ila yau, sanarwar ta ce sauran hukumomin gwamnati sun samu kudi har N1.8trn wanda hakan na daga cikin dalilin bukatar kara kasafin.
Bayan karanta wasikar, Shugaban Majalisar Dattawa ya aika bukatar ga Kwamitin Kasafin Kudi don nazari cikin gaggawa.
Ya bayyana cewa ana sa ran kammala duba kasafin kudin kafin karshen watan Fabrairun 2025, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Tinubu zai kai ziyara kasar Faransa
A baya, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairun 2025 domin zuwa ƙasar waje.
Rahotanni sun tabbatar cewa shugaba Tinubu zai shilla zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin yin wata ziyara ta ƙashin kansa.
Daga Paris, ana sa ran shugaba Tinubu zai zarce zuwa birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha a mako mai zuwa domin halartar wani taro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng