Kamfanin NORD: Nigeria ta ƙera motarta, duba hoto da bidiyo
- Kasar Najeriya ta sake samun motar da aka kera a cikinta kuma tuni bidiyon motar ya yi fice
- Dan gajeren bidiyon ya nuna irin karfin da motar ke dashi a ido da kuma kyakyawan fentin da jikin motar ke dauke da shi
- Wasu yan Najeriya da suka yi sharhi kan bindiyon sun ce ya nuna makoma mai kyau ga kasar
Yan Najeriya da dama sun gaza yin shiru bayan wani bidiyo na wata mota kirar Najeriya ta yi fice a yanar gizo.
Shugaban kamfanin da ta kera motar mai suna Nord Tank, Ajayi Oluwatobi, ya yi magana game da motar.
A rubutun da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, ya bayyana cewa musamman aka kera motar saboda yan Najeriya.
A dan takaitacen bidiyon, kamarar ta kewaya jikin motar domin ba mutane damar ganin wajenta.
An yi fentin motar da kalar bula da fari inda bamfar motar ta kasance dauke da wannan kala. Yana kuma da karfe kalar silba.
Ga martanin mutane a kasa:
@AyoOyalawo ya ce: “Wannan ya yi kyau. Ina kaunar wannan kaya da aka kera a Najeriya. Dan Allah a bari mu ga yadda za mu tura wannan gaba”
@INTERMIDIARY_NG ya ce: “Ya yi kyau sosai amma shin matsakaicin dan Najeriya zai iya siya? Babu matsakaicin dan Najeriya da zai so kashe naira miliyan 6 zuwa 8 a kan motar da aka kera a Najeriya; za su gwammaci su tuka gwanjon mota na waje. Wannan shine gaskiyar halin da ake ciki a kasarmu.”
KU KARANTA KUMA: Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin
A cewar @Bobbyk73040633, motar ta ba da ma’ana sosai.
@dashlyshair ya ce: “Ban shirya mallakar mota ba, amma ina taya Najeriya farin ciki. Daga karshe mun fara kaiwa inda ya kamata."
Kalli wani bidiyon:
A wani labari na daban, mun ji a baya cewa wani matashin saurayi dan shekara goma sha tara (19) mai suna Izunwa Justin Chinedu, wanda ya fito daga kauyne Amurie Omanze dake karamar hukumar Isu cikin jihar Imo, ya kera wata sabuwar mota.
Matashin saurayin bayan kammala kera motar tashi ya sanyawa motar suna G-Wagon, matashin yayi amfani da injin mashin da kuma tankin injin janareto wajen tada injin motar.
Bayan haka kuma saurayin yayi amfani da karafa kala-kala inda ya hada gangar jikin motar, sai dai kuma motar ya yi ta tsirara ne ba tare da ya rufe ta ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng