NNPCL: An Bude Gidan Man da Mutum zai Rika Zuba Fetur da Kan Shi

NNPCL: An Bude Gidan Man da Mutum zai Rika Zuba Fetur da Kan Shi

  • Kamfanin NNPCL ya fara ƙaddamar da famfunan mai na debi da kan ka a wasu tashoshinsa, inda direbobi za su iya zuba fetur da kansu ta amfani da manhajar waya
  • Sabon tsarin na bai wa masu abubuwan hawa damar zaɓar adadin man da suke so, su biya ta manhaja sannan su yi amfani da lambar da aka ba su wajen kunna famfon
  • NNPCL na shirin ƙaddamar da tashoshin mai masu amfani da wannan fasaha tsakanin 50 zuwa 70 a faɗin ƙasar cikin wata shida masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Kamfanin man Nigerian na NNPC ya fara ƙaddamar da tsarin zuba mai da kai a wasu tashoshinsa na sayar da man fetur.

Tsarin na bai wa masu abubuwan hawa damar sayen fetur ta manhaja tare da zuba adadin da suka biya ba tare da taimakon ma’aikacin tashar ba.

Kara karanta wannan

Wasu matasa da aka sa a kwamitin yakin zabe sun wulakanta Tinubu a gaban kowa

Gidan man zamani na NNPCL
Sabon gidan man da NNPCL ya bude a Abuja. Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Yadda za ka yi amfani da tsarin

Mataki na farko shi ne sauke manhajar NRL Fuel a waya. NNPC ya wallafa bidiyon yadda ake amfani da tsarin a shafinta na X.

Bayan buɗe manhajar, sai a danna “Fuel Purchase” sannan a zaɓi irin man da ake son saye.

Sabon tsarin yana aiki ne kawai a wasu tashoshin NNPC da aka zaɓa. Ana iya gane su ta alamar “Self-Serve” mai launin kore da ke kusa da sunan tashar.

Yadda za ka biya kuɗin man

Bayan zaɓar tashar, sai mai amfani ya shigar da adadin kuɗin da yake son kashewa wajen sayen fetur.

Daga nan zai duba adadin man da farashinsa sannan ya danna “Pay from Wallet” domin kammala biyan kuɗin.

Idan an samu nasarar biyan kuɗin, manhajar za ta samar da rasit na zamani da ke ɗauke da lambar oda, lambar amfani da tsarin kai-da-kanka da kuma lambar QR.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya saki bama bamai a Zamfara, an kashe Kachalla Gurgu

Yadda za ka zuba man da kanka

Da isa wurin famfon, mai amfani zai shigar da lambar kai-da-kanka mai lambobi takwas a na’urar famfon sannan ya danna maballin #.

Bayan an tantance lambar, sai ya ɗauki bututun zuba mai ya fara zuba fetur, inda zai samu daidai adadin man da ya biya.

Mota na shan mai a gidan mai
Ana zuba fetur a mota a sabon gidan man NNPCL. Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Ga bayanin da NNPCL ya yi a bidiyo:

A yanzu haka, kamfanin man na shirin fadada irin tashoshin zuwa sauran sassan Najeriya a cikin watanni masu zuwa.

Batun sayen hannun jarin Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar man Dangote ta amince da bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi, kamfanonin sadarwa da masu zuba jari za su iya amfani da su wajen sayen hannayen jarin kamfanin.

Kamfanin ya wallafa jerin tashoshin da aka amince da su a shafinsa na IPO, tare da gargadin masu zuba jari da su yi amfani da waɗanda aka tabbatar da su kaɗai.

Rahoto ya nuna cewa jerin wuraren da kamfanin ya fitar ya ƙunshi bankuna 20, kamfanonin fasahar kuɗi 17, kamfanonin sadarwa biyu da NGX Invest.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng