CBN Ya Bullo da Haraji Ga Abokan Huldar Bankuna, Za a Fara Cire 0.5% Idan An Tura Kudi

CBN Ya Bullo da Haraji Ga Abokan Huldar Bankuna, Za a Fara Cire 0.5% Idan An Tura Kudi

  • Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya za su fara karbar harajin kaso 0.5% daga kudaden da abokan hulda ke turawa
  • Babban bankin Najeriya (CBN) ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin, tare da kakaba tarar kaso 2% idan ba a biya harajin ba
  • A cewar CBN, umarnin zai fara aiki nan da makonni biyu kuma za a rika kiran kudin harajin a matsayin 'kudin tsaron yanar gizo'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara karbar harajin kaso 0.5% domin turawa 'asusun tsaron yanar gizo.'

Za a rika cire kudin ne da zarar abokan huldar bankunan sun tura kudi daga asusunsu ta intanet, in ji jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Bankuna sun dawo cire kaso 2% idan abokan hulda za su ajiye sama da N500,000

CBN ya bullo da sabon haraji na 'tsaron yanar gizo'
CBN ya umarci bankuna su fara cire harajin 0.5% daga abokan huldarsu domin tsaron yanar gizo. Hoto: @cenbank
Asali: Facebook

CBN ya ba bankuna umarnin cire 0.5%

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ke dauke da sa hannun daraktan kula da tsarin biyan kudi Chibuzor Efobi da Haruna Mustafa, daraktan tsare-tsare na kudi a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ba da umarnin ne ga bankunan kasuwa, manyan ƴan kasuwa, bankunan da ba su karbar kudin ruwa da bankunan biyan kuɗi da na intanet, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

CBN ya ce wannan umarnin zai fara aiki nan da makonni biyu kuma za a bayyana kudin harajin a matsayin ‘Cybersecurity Levy’, watau 'kudin tsaron yanar gizo.'

Abin da za a yi da kudin harajin

Channels TV ya ruwaito cewa babban bankin ya ce cirewa da tattara harajin kudin tsaron ya biyo bayan aiwatar da dokar aikata laifuffuka a yanar gizo da aka sabunta a 2024.

Kara karanta wannan

Lamari ya lalace; Gwamantin jihar Kano ta saka dokar ta baci a kan harkar ilimi

CBN ya ce za a mika kudin ne ga asusun tsaron yanar gizo na kasa, wanda ofishin hukumar NSA zai gudanar.

Babban bankin ya ce rashin saka harajin kudin wani laifi ne da ka iya jawo tarar sama da kashi 2% na kudin ribar shekara da bankuna ko cibiyoyin hada-hadar kudi suka samu.

CBN ya magantu kan tsadar kayayyaki

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito babban bankin Najeriya (CBN) ya zargi gwamnatin tarayya da 'yan majalisu da haifar da hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

GwamnanCBN, Olayemi Cardoso, ya ce sayan kayan abinci da gwamnati da 'yan majalisu suka yi domin rabawa talakawa ya jawo tsadar kayayyakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel