NiMet: Za a Tsula Ruwan Sama a Kano, Gombe da Wasu Jihohin Arewa a Yau

NiMet: Za a Tsula Ruwan Sama a Kano, Gombe da Wasu Jihohin Arewa a Yau

  • Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashe game da yadda yanayi zai kasance a Najeriya a ranar 30 ga Yunin shekara 2026
  • Ta ce za a iya yin tsawa da ruwan sama a sassa da dama na jihohin Arewa, yayin da za a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi da yamma
  • A jihohin Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce ana sa ran samun gajimare da safiya kafin tsawa da ruwan sama su mamaye yankin da yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa ta fitar da sanarwa game da yankunan da za a samu ruwan sama a ranar Talata, 30 ga Yunin 2026.

A hasashen da NiMet ta yi, ta sanar da cewa za a yi ruwan sama a jihohi da dama a Arewacin Najeriya ciki har da Gombe.

Ana ruwan sama a Gombe
Yara na wasa a ruwan sama a Nafada a jihar Gombe. Hoto: Salmanu Muhammad
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da hasashen ne a cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a daren Litinin, 29 ga Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fitar da fiye da Naira tiriliyan 2, za a zuba manyan ayyuka a jihohi 10

Jihohin da za a yi ruwan sama

Hasashen NiMet ya nuna cewa za a yi tsawa sosai a jihohin Arewa da dama da safe yayin da ruwan sama zai ƙaru da yamma.

Hasashen ya nuna cewa ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu sassan jihohin Borno, Adamawa da Taraba.

Ta kara da cewa ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu sassan jihohin Bauchi, Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto, Yobe, Gombe da Kebbi.

NiMet ta ce hakan na nufin fara yini da yanayi mai ruwa a wasu sassan Arewa maso Gabas, kafin tsawa da ruwan sama su bazu zuwa wasu yankuna da yamma.

Hasashen ruwa a Arewa ta Tsakiya

NiMet ta ce ana sa ran yanayi mai yawan gajimare, tare da yiwuwar tsawa da ɗan ruwan sama a wasu sassan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nasarawa da Benue.

Daga rana zuwa yamma kuwa, ta ce ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a dukkan yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Katsina ta ce da aka kama shugabannin ƴan ta'adda a filin jirgi

Ta bukaci mazauna yankin su yi tsammanin ƙarin gajimare da rana, kafin tsawa da ruwan sama su mamaye yankin da yamma.

Me zai faru a jihohin Kudu?

A jihohin Kudu da safe, ana sa ran tsawa tare da ɗan ruwan sama a wasu sassan jihohin Ondo, Ogun, Edo, Legas, Rivers, Delta, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.

Daga rana zuwa yamma kuwa, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a dukkan yankin Kudu, tare da yiwuwar ambaliyar ruwa a yankunan bakin teku, musamman a jihohin Ogun, Ondo, Legas, Rivers, Bayelsa, Delta, Cross River da Akwa Ibom.

Yadda ruwan sama ke sauka
Yadda aka yi ruwa a jihar Gombe, Hoto: Muhammad Hassan
Source: Facebook

Gargadin NiMet ga 'yan Najeriya

NiMet ta ce iska mai ƙarfi na iya kaɗawa kafin fara tsawa saboda haka masu abubuwan hawa su yi taka-tsantsan yayin ruwan sama.

Ta yi gargadi da a guji tuƙi ko tafiya cikin ruwan a lokacin ambaliya kuma kada a nemi mafaka a ƙarƙashin dogayen bishiyoyi yayin tsawa.

An nemi kamfanonin jiragen sama su riƙa samun rahoton yanayin filayen jiragen sama daga NiMet domin tabbatar da tsaro da ingancin zirga-zirgar jirage.

Kara karanta wannan

Fada zai dawo: Trump ya yi gargadi mai tsauri kan Iran duk da maganar sulhu

Jihohin da za a fi samun ruwa

A wani rahoton, mun kawo muku cewa hukumar hasashen yanayi ta NiMet ta fadi jihohin da za su fi samun ruwan sama a damunar shekarar 2026.

A hasashen da NiMet ta yi, ta bayyana cewa Gombe, Kwara, Kogi da Taraba na cikin jihohin da za su fi samun ruwan sama a bana.

Haka zalika Enugu, Ebonyi, Anambra, Nasarawa na cikin jihohin, inda ta bukaci manoma su zauna cikin shiri kafin damuna ga kankama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng