Rasha da China Sun Hana Amurka Daukar Mataki kan Nukiliyar Iran
- Mambobin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) sun gudanar da kuri'ar mika batun nukiliyar Iran zuwa ga Kwamitin Tsaron UN
- Wannan shine karon farko da aka tura Iran gaban kwamitin tsaron a cikin shekaru 20 sakamakon zarginta da kin biyayya ga ka'idojin nukiliya
- Bayan matakin da China da Rasha suka dauka, Iran ta yi Allah wadai da hakan inda ta bayyana shi a matsayin matakin siyasa maras amfani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre me a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Vienna – Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta gudanar da kuri'a a ranar Laraba inda ta yanke shawarar mika shari'ar nukiliyar Iran zuwa ga kwamitin tsaron sakamakon "kin biyayya" ga ka'idojin da aka gindaya.
Matakin dai na zuwa ne sakamakon hana jami'an hukumar samun damar gudanar da bincike a cibiyoyin nukiliyar kasar tun bayan rikicin kwana 12 da ya barke tsakaninta da Isra'ila tare da goyon bayan Amurka a watan Yunin 2025.

Source: Getty Images
Al Jazeera ta ruwaito cewa an amince da wannan kuduri ne bayan samun kuri'u 23 daga kasashe mambobi, yayin da kasashe uku suka ƙi amincewa, sannan kasashe takwas suka janye jikinsu.
Rasha da China sun magantu
Kasashen Rasha, China da Nijar ne suka kaɗa kuri'ar ƙin amincewa da kudurin wanda kasashen Biritaniya, Faransa, Jamus da Amurka suka gabatar gaban kwamitin gudanarwa na hukumar.
Matakin dai yana buƙatar Darakta Janar na hukumar IAEA da ya mika rahoton rashin biyayyar Iran ga Kwamitin Tsaro da kuma Babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ya rubuta cewa:
"Kudurin yana nuna alhini mai tsanani game da ci gaba da kin biyayyar Iran ga kudurori, sannan yana sake kiran kasar da ta gaggauta sake matsayarta tare da shiga tsakani tsakanin kasashe cikin gaskiya ba tare da gindaya sharuda ba."
Martanin Iran kan kudurin
Ita kuwa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gaggauta yin Allah wadai da kudurin, inda ta bayyana shi a matsayin matakin da aka ɗauka sakamakon matsin lamba na siyasa daga Amurka da kawayenta.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun mamayi mutane a kananan hukumomi 2, sun kashe bayin Allah da dama
Yahoo News ta wallafa cewa wakilin kasar Iran a hukumar IAEA, Reza Najafi, ya bayyana ta gidan talabijin din kasar cewa matakin ba shi da wani tushe na shari'a kuma ba zai haifar da wani sakamako mai kyau ba.

Source: Getty Images
Babban darektan IAEA, Rafael Grossi, ya bayyana cewa ba wa jami'ansu damar shiga manyan cibiyoyin nukiliyar Iran zai taimaka wajen maido da amincewar kasashen duniya game da tsarin nukiliyar kasar na zaman lafiya.
Iran ta kai hari kan sojin Amurka
A wani labarin, kun ji cewa an lalata jiragen saman yakin Amurka da dama sakamakon harin da dakarun Iran suka kai kan sansanin sojin saman Muwaffaq Salti da ke kasar Jordan daga daren Talata zuwa Laraba.
Kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito daga majiyoyi na kusa, kimanin jiragen yaki nau'in F-15 guda takwas ne suka sami ƙananan lalacewa yayin da aka lalata fiffiken jirgi mai saukar ungulu nau'in A-10 Thunderbolt.
Rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta tabbatar da kaddamar da harin a matsayin martani ga matakin da Amurka ta dauka na kai hari kan jiragen man fetur guda biyar na Iran.
Asali: Legit.ng
