Na fi kowa cin WAEC 1976: Abokin takarar Atiku ya magantu kan batar takardunsa

Na fi kowa cin WAEC 1976: Abokin takarar Atiku ya magantu kan batar takardunsa

  • Gwamna Ifeanyi Okowa ya bayyana rahotannin kafafen yada labarai game da bacewar sakamakonsa na jarrabawa a matsayin wata rashin fahimta da ganganci
  • Gwamnan na jihar Delta ya ce shi dalibi ne da ya samu sakamako da maki mai kyau a jarrabawar da ya rubuta ta WAEC
  • Okowa wanda shi ne dan takarar mataimakin dan takarar shugaban kasa a PDP ya kara da cewa kusan dukkanin jami’o’in kasar nan ne suka ba shi gurbin karatu a bisa irin kwazon da ya nuna a WASC

Ozoro, Isoko North LGA - Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta, ya karyata rahotannin da ke cewa ba shi da takardar sakamakon kammala karatun sakandare na WASC.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana cewa shi dalibi ne mai kwazo a matakin sakandare, inji rahoton jaridar The Nation.

Okowa ya magantu oan satificate na WAEC
Ban san inda WAEC dina take ba: Abokin takarar Atiku ya magantu kan batun batar takardunsa | Hoto: IAOkowa
Asali: Twitter

Gwamna Okowa ya kara da cewa, shi ne ya fito a matsayin dalibi na biyu mafi kwazo a jarrabawar da ya rubuta a 1976.

Kusan dukkan jami'o'in Najeriya ne suka ba ni gurbin karatu - Okowa

Okowa wanda ya yi magana a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Delta, Ozoro da ke karamar Hukumar Isoko ta Arewa, ya kuma ce kusan daukacin Jami’o’in kasar nan ne suka ba shi gurbin karatu, bisa la’akari da yadda sakamakonsa na WASC da HSC suka yi kyau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar gwamnan na jihar Delta, rahotannin kafafen yada labarai game da bacewar sakamakonsa “rashin fahimta ne da gangan da kuma siyasar da ba ta da amfani.”

Kalamansa:

“A kan batun takardar satificet dina, ina ganin kuskure ne. Mutane suna kokarin mai da komai siyasa.
“Eh, na satifiket din WAEC dina ya bata amma ina da bugunsa daga Kwalejin Edo da ke birnin Benin, wanda ya bayyana karara cewa ina da sakamako mai kyau a kowane fanni.

Ya kuma bayyana cewa, sakamakon da ya samu duka 'B' a darussan da zana jarrabawar akai.

“Ba na alfahari ba amma yana da wahala a samu irin wannan maki a babbar makarantar sakandare a lokacin.
“Sakamakon karatuna na sakandare shi ne na biyu mafi kyau a kasar a 1976 lokacin da na gama. Don haka, jami'o'i da yawa sun bani gurbi ta Telegram kamar yadda a wancan lokacin kuma dole ne in fara zabar abin da zan karba.
“Tabbas, a fili yake cewa na gama karatun likitanci a Jami’ar Ibadan. Ina da shekara 21 a lokacin da wasu watanni; Ban kai shekara 22 ba.’’

‘Yan kasuwan Sokoto sun bar APC sun kama PDP bisa saba alkawuran APC

'Yan kasuwa a Sokoto sun fice daga APC zuwa PDP saboda rashin cika alkawura da APC ta yi wa Kungiyar matasan ‘yan kasuwan jihar Sokoto.

Sun koma PDP, jam'iyya mai mulki a jihar domin marawa tafiyar jam'iyyar baya a zabuka da ke tafe a 2023.

Rahoton Daily Trust ya ce, ’yan kasuwar da suka yi tir da kasancewarsu a jam’iyyar APC sun yi ficewarsu daga cikinta ne a cibiyar tarihi da ke Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel