Gwamnatin Najeriya za Ta Fara Tura Kyautar Data domin Shiga Intanet

Gwamnatin Najeriya za Ta Fara Tura Kyautar Data domin Shiga Intanet

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ɗaliban Najeriya za su fara samun 100MB kyauta a kowace rana daga 1 ga Oktoba 2026
  • Tsarin zai fara ne da ɗaliban manyan makarantun sakandare na gwamnati da jami'o'i, kafin a faɗaɗa shi zuwa sauran nau'o'in masu koyo
  • Gwamnati ta ce za a bai wa ɗalibai damar shiga shafukan yanar gizo da dandalolin ilimi da aka amince da su ba tare da cire kuɗin data ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin tarayya ta sanar da fara shirin bai wa ɗaliban Najeriya 100MB na bayanan intanet kyauta a kowace rana daga ranar 1 ga Oktoba 2026.

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya sanar da ranar fara shirin ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da shirin samar da damar shiga shafukan ilimi da abubuwan koyarwa kyauta a Abuja.

Kara karanta wannan

2027: An fatattaki 'yan ADC a Kaduna, jam'iyyar ta fitar da gargadi

Dr Tunji Alausa a wajen taro
Ministan ilimin Najeriya, Dr Tunji Alausa. Hoto: Federal Ministry of Education
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ce za ta aiwatar da shirin tare da haɗin gwiwar kamfanonin sadarwa da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya.

Alausa ya ce:

“Bari in bayyana sirrin. Za a samar da wannan dama ga ɗaliban Najeriya daga 1 ga Oktoba 2026.”

Daliban da za su fara amfana

A karkashin tsarin, kamfanonin sadarwa da suka shiga shirin za su bai wa masu amfana 100MB na data kyauta kowace rana.

Za a iya amfani da data ɗin ne wajen shiga shafukan yanar gizo da dandalolin ilimi da gwamnati ta amince da su.

Ministan ya ce za a fara ne da ɗaliban manyan makarantun sakandare da na manyan makarantun gaba da sakandare, kafin daga baya a faɗaɗa shirin zuwa sauran masu koyo.

Alausa ya ce tsadar data ta zama babban cikas ga ilimin zamani, musamman ga yaran da suka fito daga gidaje masu ƙaramin ƙarfi.

Gwamnati za ta sa ido

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na aiki kan matakan da za su tsara yadda yara ‘yan ƙasa da shekaru 16 za su samu damar amfani da intanet.

Ya ce za a fitar da ƙarin bayani kan matakin daga baya, inda ya jaddada cewa abubuwan ilimi da ake bai wa yara dole su kasance masu dacewa da shekarunsu, ingantattu kuma masu aminci.

Vanguard ta wallafa cewa ya ƙara da cewa gwamnati na faɗaɗa tsarin zamani a fannin ilimi ta hanyar wasu tsare-tsaren tattara bayanan makarantu da ɗalibai.

Ya ce an riga an gano tare da sanya alamar wurin fiye da makarantu 240,000 a faɗin ƙasar, yayin da ake mayar da ƙidayar makarantu ta shekara zuwa tsarin zamani.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kwamishiniyar Zartarwa ta NCC mai kula da Hulɗa da Masu Ruwa da Tsaki, Rimini Makama, ta ce miliyoyin ɗalibai ba sa iya amfani da dandalolin koyarwa na zamani saboda tsadar data.

An yaba da shirin NELFUND

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kashim Shettima, ya bayyana shirin NELFUND da gwamnati ta kafa a matsayin wani gagarumin shiri da ya rage wa marasa ƙarfi matsin tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya

Shettima ya ce gwamnatin ta mayar da NELFUND wani muhimmin shiri na rage gibin tattalin arziƙi da kuma samar da damar samun ilimi ga ɗaliban Najeriya.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, lokacin da ya karɓi tawagar shugabannin Jami'ar Abuja ƙarƙashin jagorancin, Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng