Kaduna: Sarkin Zazzau Ya Amince Na Naɗin Ɗansa Babban Muƙami a Masarautar

Kaduna: Sarkin Zazzau Ya Amince Na Naɗin Ɗansa Babban Muƙami a Masarautar

  • Bayan rasuwar Walin Zazzau a jihar Kaduna, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya nada dansa domin maye gurbin marigayin
  • Sarkin ya nada Abdullahi Nuhu Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau bayan rasuwar Injiniya Aminu Umar a makon da ya gabata
  • Mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma'a Asabar 19 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya amince da nadin dansa mukami a masarautar.

Sarkin ya nada dan nasa, Abdullahi Ahmed Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi nade-nade a hukumomin SEC da NAICOM, 'Yan Arewa sun samu shiga

Sarkin Zazzau ya amince da nadin ɗansa a muhimmiyar sarauta a Kaduna
Sarkin Zazzau a jihar Kaduna ya nada ɗansa, Abdullahi Bamalli sarautar Walin Zazzau. Hoto: Aliyu Abdullahi Kwarbai.
Asali: UGC

Yaushe aka yi nadin sarautar a Zazzau?

Nadin matashin na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Injiniya Aminu Umar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanar da mutuwar Injiniya Aminu Umar ne a ranar Lahadi 14 ga watan Afrilu bayan ya sha fama da gajeruwar jinya.

Sanarwar ta ce sarautar Walin Zazzau ta na mataki na uku daga cikin sarautun Hakimai bayan sarautar Madaki da Magajin Gari.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar a shafin Facebook.

Kwarbai ya ce kakan Abdullahi Bamalli na uku ya taba rike sarautar Walin Zazzau wanda aka fi sani da Halliru.

Sanarwar ta kara da cewa Sarkin ya kuma amince da nadin Injiniya Sani Galadima wanda kani ne ga marigayi tsohon Walin Zazzau a matsayin Yariman Zazzau.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar tsohon dan Majalisar Tarayya a Kwara, Sanata ya tafka babban rashi

Hakan ya biyo bayan nada tsohon Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru wanda Sarkin ya ba muƙamin sabon Madakin Zazzau.

An yi babban rashi a masarautar Zazzau

A baya, kun ji cewa Allah ya karbi rayuwar Injiniya Aminu Umar, Hakimin Ikara kuma Walin Zazzau da ke jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da wannan babban rashi, Abdullahi Aliyu Kwarbai, kakakin masarautar Zazzau, ya ce marigayin ya halarci dukkannin bukukuwan Sallah.

Kwarbai ya ce marigayi Injiniya Umar ya halarci Hawan Daushe da Hawan Daba da aka yi a Zariya a ranar Juma'a 12 fa watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel