Najeriya ta fi kowace kasa tsadar 'Data' a duniya, wani binciken kasashe 85 ya bayyana

Najeriya ta fi kowace kasa tsadar 'Data' a duniya, wani binciken kasashe 85 ya bayyana

Farashin Data na da matukar tsada a Najeriya da kasar ce ta gaba cikin binciken da aka gudanar kan kasashe 85 a fadin duniya, Premium Times ta gani a wani bincike.

A binciken da Surshark Press, wani kamfanin a kasar Amurka ya saki ranar Litinin, an samu cewa Najeriya na kasa da kasar Kolombiya da Honduras wajen arhan 'Data'.

"Najeriya ce kasa maras rahusan Data a fadin duniya. Tana kasa da Kolumbiya da Honduras wajen rahusan Data," Jawabin yace.

A salon da kamfanin tayi amfani da shi wajen binciken, an lura da tsarin 'data' mafi arha a kowace kasa.

A kan ingancin yanar gizo kuwa, Najeriya ta zo na 81 cikin kasashe 85.

An gudanar da binciken kan abubuwa gida biya: Saukin Data, ingancin yanar gizo, kayan alatun yanar gizo, gwamnatin zamani, da tsaron yanar gizo.

A nahiyar Afrika, rahoton ya ce yayinda Najeriya ta wuce kasar Algeria, ta na bayan Afrika ta kudu, Kenya , Moroko da Tunisiya.

KU KARANTA: Na cika alkawarina na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya - Buhari

Najeriya ta fi kowace kasa tsadar 'Data' a duniya, wani binciken kasashe 85 ya bayyana
dataa
Asali: Depositphotos

A bangare guda, mun kawo muku rahoton cewa Hukumar sadarwan Najeriya a karshen makon da ya gabata ta yi kira ga kamfanonin sadarwa su rage kudin katin shiga yanar gizo da akafi sani da 'Data' saboda su ma an rage musu kudin lasisin birne wayoyinsu a jihohin Najeriya

Shugaba hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta, ya bayyana hakan yayainda yake jawabi ga mahalartan taron yanar gizon majalisar masu amfani da layukan sadarwa, a hedkwatar NCC dake Abuja, The Nation ta ruwaito.

Danbatta ya ce dubi ga irin hobbasan da gwamnatin Najeriya tayi na ganin cewa an ragewa kamfanonin sadarwan kudin lasisin birne wayoyinsu a jihohi zuwa kasa da N145 ga mita yayinda wasu jihohi suka yafe kudin gaba daya, ya zama wajibi su dan yunkura domin nuna godiya .

"Hukumar na sa ran cewa dubi da ragin kudin lasisin birne wayoyin da aka samu, wanda zai rage kudin da kamfanonin sadarwa zasu rika kashewa, ya kamata su nuna godiya ta hanyar rage kudin abubuwa musamman 'data' ga yan Najeriya," Ya ce

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel