Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki

Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki

  • Na Allah basu kare ba a doron kasa, iyalin mamaci sun cika masa wasiyyar da yayi na mayar da makudan kudi asusun gwamnatin Yobe
  • Mamacin yace tsawon shekarun da yayi aiki, bai cika sharadin zuwa ofis sau biyar a mako ba saboda tsufa da rashin lafiya
  • Saboda haka ya yi lissafin ranakun da yayi fashi zuwa kimanin shekaru 11 kuma yayi wasiyyar a mayar kudin asusun gwamnati

Iyalin marigayi Baba-Aji Mamman sun bayyana cewa sun mayar da kudi N11 million asusun gwamnatin jihar Yobe saboda rashin zuwa aikin mahaifinsu lokacin da yake raye.

Marigayin ya kasance tsohon ma'aikacin hukumar samar da wutan lantarki a karkara na jihar Yobe.

A sanarwan da iyalinsa suka yi ranar Laraba kuma aka wallafa a jaridar Daily Trust, sun nemi gafarar al'ummar jihar da ma'aikatar da yayi aiki.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

A cewar sanarwar, marigayin wanda ya rasu ranar 28 ga Maris, 2020 da kansa ne ya bukaci su yi hakan kafin mutuwarsa a wasiyyarsa.

Ya ce su mayar da albashin shekara 11 asusun gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki
Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki
Asali: Getty Images

Me yasa yayi haka?

Iyalin sun bayyana cewa bai samun daman zuwa aiki a dukkan ranakun aiki saboda tsufa da rashin lafiya.

Jawabin yace:

"Marigayi AlhajiBaba-Aji Mamman ya rasu ranar 28 ga Maris, 2020. Allah ya jikansa Amin."
"A matsayin ma'aikatan hukumar, saboda tsufa, rashin lafiya da wasu dalilai, ya kan je ofis sau biyu ko sau uku maimakon sau biyar da aka shardanta."
"Marigayi Baba-Aji Mamman ya bada umurnin a mayar da kudin albashin kimanin shekaru 11 wanda shine N11,000,000 asusun gwamnatin jihar."
"Iyalin sun tattara kudi kuma sun biya asusun gwamnatin jihar na bankin Access mai lamba 0765651829."

Kara karanta wannan

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

"Allah ya baku daman gafarta masa da kuma yi masa addu'an Allah ya bashi Aljannah firdaus."

Asali: Legit.ng

Online view pixel