Iran Ta Fuskanci Koriya Ta Kudu, Ta Mata Gargadi kan Hada kai da Amurka

Iran Ta Fuskanci Koriya Ta Kudu, Ta Mata Gargadi kan Hada kai da Amurka

  • Iran ta gargadi Koriya ta Kudu cewa za ta fuskanci “mummunan sakamako” idan ta tura sojojinta cikin Tekun Farisa da Mashigar Hormuz
  • Gargadin na zuwa ne yayin da ake rahoton cewa Seoul na duba yiwuwar bayar da gudunmawar soji wajen tabbatar da zirga-zirga a mashigar
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce shigar Koriya ta Kudu yakin zai iya zama kamar goyon bayan Amurka, wadda Tehran ke zargi da kai mata hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran – Iran ta gargadi Koriya ta Kudu kan yiwuwar fuskantar “mummunan sakamako” idan ta shiga aikin soji a Tekun Farisa da Mashigar Hormuz, yayin da ake samun rahotannin cewa Seoul na nazarin tura jami’an tsaro ko kayan aikin soji yankin.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce Iran na daraja dangantakarta da Koriya ta Kudu da ta shafe sama da shekaru 64.

Kara karanta wannan

Amurka ta kaddamar da sababbin hare hare kan jirgin Iran

Shugaban kasar Iran a wajen taro
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Anadolu Agency ta wallafa cewa Koriya ta Kudu ya ruwaito cewa Seoul na ci gaba da tuntubar wasu kasashe kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da kuma batun tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin walwala a Mashigar Hormuz.

Gargadin Iran ga Koriya ta Kudu

Baqaei ya ce dangantakar Iran da Koriya ta Kudu ta kasance bisa mutunta juna tsawon shekaru, yana mai jaddada cewa Tehran na ba wannan alaka muhimmanci.

Sai dai ya ce a halin yanzu al’ummar Iran na kare kansu daga abin da ya kira “ta’addancin Amurka” da kuma laifuffukan yaki da Amurka ke aikatawa kan mata da yara.

Ya ce duk wani kasancewar sojojin wata kasa ko shiga cikin ayyukan soja a Tekun Farisa da Mashigar Hormuz za a dauke shi a matsayin goyon bayan kai tsaye ga wanda Iran ke zargi da kai mata hari.

Ya wallafa a X cewa:

“Ba makawa za a dauki hakan a matsayin goyon baya kai tsaye ga wanda ya kai hari, kuma zai haifar da mummunan sakamako,”

Kara karanta wannan

Yadda aka jefar da jarirai a kango cikin ban tausayi bayan an haife su a Abuja

Ya kuma bukaci kasashe masu cin gashin kansu da masu alhakin kasa da su guji mika wuya ga matsin lamba da barazanar Amurka.

Seoul na tuntubar kasashe

Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Kudu ta ce tana ci gaba da tuntubar kasashen duniya, ciki har da kasashen da abin ya shafa, domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.

Ta ce tana kuma kokarin tabbatar da samun damar dukkan jiragen ruwa, ciki har da na Koriya ta Kudu, su ratsa Mashigar Hormuz cikin walwala.

Lee Jae Myung a wajen taro
Shugaban kasar Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar rahoton, gwamnatin Koriya ta Kudu ta ci gaba da bude hanyoyin diflomasiyya da Iran yayin da ake ci gaba da nazarin halin da ake ciki.

Rahoton ya ce Shugaban Amurka Donald Trump na kara matsa wa Koriya ta Kudu lamba domin ta bayar da gudunmawar soji ga kokarin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz.

Jirgin ya fadi a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata bayan wani jirgin dakon kaya na Boeing 767-300 na Amazon ya yi hatsari a filin jirgin Miami.

Kara karanta wannan

DSS ta yi magana kan zargin sanata da taimakon 'yan ta'adda

Jirgin Amazon Prime Air ya yi hatsarin ne jim kadan kafin karfe 2:00 na rana ranar Lahadi, bayan ya kasa tsayawa kan titin saukar jiragen sama ya wuce iyakarsa.

Jirgin ya bugi motoci da dama a wata hanya da ke bayan filin jirgin, lamarin da ya haddasa gobara da malalar man fetur, yayin da hukumomin jiragen sama na Amurka suka dakatar da zirga-zirgar jirage.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng