Yan Firamare Sun Danne Dalibi, Sun Yi Masa Kaciya a Bandakin Makaranta
- Wani yaro mai shekaru 11 a Afirka ta Kudu ya zargi wasu ɗalibai huɗu da tilasta masa kaciya a makaranta
- Rahotanni sun ce ɗaliban aji bakwai sun riƙe yaron, suka yanke fatar gabansa, sannan suka yi masa barazanar ka da ya tona asirinsu
- Mahaifiyar yaron ta kai ƙara ga ’yan sanda, yayin da rundunar ’yan sandan Afirka ta Kudu ta ce tana binciken lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pretoria, South Africa - Hukumomi a kasar Afirka ta Kudu sun nuna damuwa game da cin zarafin wani yaro dan firamare.
An zargi wasu ɗalibai huɗu da jan wani yaro mai shekaru 11 zuwa bayan gida a makaranta, inda suka yi masa kaciya da ƙarfi.

Source: Getty Images
Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba a Afirka ta Kudu, yayin da yaron yake lokacin hutu.
Yadda yaran firamare suka yi wa dalibi kaciya
Yaron, wanda ke aji na biyar, an kai masa hari a makarantar firamare ta Sinqobil da ke Soshanguve, Arewacin Pretoria.
Rahoton ya ce wasu ɗalibai huɗu da ke aji na bakwai sun riƙe yaron, sannan suka yanke fatar da ke rufe kan al’aurarsa.
Majiyoyi sun ce ɗaliban sun yi wa yaron barazanar kada ya gaya wa kowa abin da suka yi masa.
Bayan harin, yaron ya koma gida, amma bai bayyana wa mahaifiyarsa abin da ya faru nan take ba.
Daga baya, mahaifiyarsa ta lura cewa yana tafiya ba kamar yadda ya saba ba, sannan ya koka da matsanancin ciwo.
Mahaifiyar, wadda ba a bayyana sunanta ba domin kare sirrin ɗanta, ta kai shi wurin likita domin samun kulawa.
Ta shaida cewa daga baya ɗanta ya nuna mata al’aurarsa da ta kumbura, sannan ya bayyana mata abin da ya faru.
Ta ce:
“Daga nan ya nuna min al’aurarsa da ta kumbura, sai na garzaya da shi wurin likita, inda muka gano cewa ɗalibai huɗu sun yi masa kaciya.
"Ɗana ya ce sauran yaran sun riƙe shi a bayan gidan makaranta yayin hutu, suka ɗaure jan zare a al’aurarsa.
"Sannan suka yanke fatar da ke rufe kan al’aurarsa. Ɗana ya ce ɗaliban aji bakwai ne, kuma sun yi masa barazanar duka idan ya gaya wa kowa, yanzu na shigar da ƙara a matsayin shari’ar laifi.”

Source: Getty Images
Abin da mahaifiyar yaron ke cewa
Mahaifiyar ta tabbatar da cewa ta shigar da ƙara a kan lamarin, domin a binciki abin da ya faru da ɗanta.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Afirka ta Kudu, Kyaftin Tintswalo Sibeko, ya ce ana binciken lamarin a matsayin hari da nufin jikkata mutum sosai.
Sibeko ya ce:
“Sashenmu na kula da tashin hankalin iyali, kare yara da laifukan lalata yana gudanar da bincike, kuma ba a kama kowa ba a wannan mataki.”

Kara karanta wannan
Minista ya kare Tinubu kan yadda gwamnoni ke kashe kudaden tallafin mai a Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta Gauteng ta ce ’yan sanda ne ke binciken lamarin, kuma sakamakon binciken zai tantance matakin da ma’aikatar za ta dauka.
Mataimakin shugaban makarantar, George Mahlangu, ya bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali, yana cewa makaranta ya kamata ta kasance wuri mai aminci.
Rahotanni sun ce daga baya ’yan sanda sun kai yaron makarantar domin ya nuna musu ɗaliban da ake zargi da kai masa harin.
Hukuncin yi wa mata kaciya a Najeriya
A baya, an ji cewa Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa ta bayyana hukuncin da zai shafi duk wanda ya yiwa mata kaciya a Najeriya.
Ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su isar da sakon ga dukkan wadanda bai riskesu ba domin kaucewa aikata laifin.
Bayanan na NAPTIP ya biyo bayan tambaya ce da wani mai amfani da kafar sada zumunta ya mata a kafar X.
Asali: Legit.ng

