Kotu Ta Tabbatar da Daurin Shekaru 490 da Aka Yanke wa Tsohon Jami’in Gwamnati

Kotu Ta Tabbatar da Daurin Shekaru 490 da Aka Yanke wa Tsohon Jami’in Gwamnati

  • Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara karkashin Mai Shari'a Muhammed Danjuma sun yi watsi da ɗaukaka ƙarar Robery Orya
  • Hukumar EFCCta gurfanar da shi a kan zargin karya, damfara, da kuma yaudarar samun kudi ta hanyar bogi a NEXIM
  • Kodayake kotun ta daure shi shekaru 10 a kowanne laifi daga cikin laifuffuka 49, duka daurin za su tafi ne a lokaci guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara mai zama a garin Abuja ya tabbatar da hukuncin daurin da alkali ta yanke wa Robert Orya.

Mista Robert Orya ya shiga matsala ne bayan ya shugabancin bankin NEXIM tun daga 2009 har zuwa farkon shekarar 2016.

Robert Orya
Wasu mutane da ake shari'a da su a Najeriya da tsohon shugaan NEXIM, Robert Orya Hoto: Getty Images/Economic and Financial Crimes Commission Nigeria
Source: UGC

NEXIM: Kotun daukaka kara ta ba EFCC gaskiya

Kotun daukaka kara ta samu Orya da laifuffukan da ake tuhumarsa da aikata wa, ta tabbatar masa da dauri a cewar Business Day.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta shiga Aso Rock ta dauke ma’aikacin da ya yi aiki da shugabannin kasa 3

Alkalai ba su samu kuskure a hukuncin kotun tarayya na Abuja ba wanda ya kama shi da aikata laifuffuka 49 da EFCC ke tuhumarsa.

Kowane laifi yana dauke da hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali a Najeriya, kenan ya tara laifuffukan shekaru 490 a tare.

Robert Orya ya yi wa'adi 2 a bankin NEXIM

Mista Orya ya shugabanci bankin shigo da fita daga kaya zuwa ketare na tsawon shekaru kusan bakwai a birnin tarayya Abuja.

Marigayi Umaru Yar’Adua ya fara nada shi a Agustan 2014, bayan wa’adinsa ya kare sai Goodluck Jonathan ya sabunta sbi a 2014.

Orya ya bar bankin NEXIM ne a Fubrairun 2016 da ya kammala duka wa’adinsa, a lokacin marigayi Muhammadu Buhari ya shiga ofis.

Kotu ta yanke wa Orya daurin shekaru 490

Shekaru bayan ya bar ofis, Daily Trust ta rahoto cewa hukumar EFCC ta yi karar shi, ana zargin ya yai awon gaba da N2.4bn daga bankin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

A 2021 lauyoyin EFCC suka tuhume shi da zargin sata, damfara da amfani da bayan karya, aka shigar da kara gaban wani kotun tarayya.

Alkalin kotun, F.E. Messiri ta same shi da laifi, ta yanke masa hukuncin dauri a gidan gyaran hali, amma Orya bai gamsu da hukuncin ba.

Hukuncin daurin shekaru 490 bai canza ba

Wannan karo ma lamarin bai canza zani ba, The Cable ta kawo labarin yadda alkalan kotun daukaka kara suka gamsu da aikin F.E. Messiri.

Mai shari’a Muhammed Danjuma da wasu alkalai biyu; Ntong Ntong da Ele Enenche suka sake zartar da wannan hukunci a birnin Abuja.

Alkalan sun duba shari’ar mai lamba FSC/SC/CS/487/2021, sun kuma ga cewa kotun tarayya ba ta yi wani kuskure wajen sauraron karar ba.

Danjuma, Ntong da Enenche duk sun hadu wajen watsi da karar tsohon shugaban bankin NEXIM, suka kuma ba lauyoyin EFCC gaskiya.

Ginin mutane sun zama makarantun gwamnati

EFCC ta bayyana cewa wata jami'ar kudi da kotu ta karbe daga barayin gwamnati ta koma ta gwamnati a Kaduna kuma har an soma karatu.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin Tinubu za ta daure daliban da suka kasa biyan bashin NELFUND?

Jami'ar NOK mai zaman kanta wadda aka kwato saboda mallakarta ta hanyar da ba ta dace ba ta zama cikin Jami'ar Kimiyya ta Tarayya (FUASK).

Akwai alamun EFCC ta mayar da jami’ar Abubakar Malami da ta ƙwace saboda sata zuwa na gwamnatin tarayya don ilmin yaran talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng