‘Suna Neman Raba Ni da Sarauta’: Sarki Ya Roki Gwamna Ya Kawo Masa Dauki
- Sarkin Aresaadu na Iresaadu, Oba Abraham Adeyeye Oyerinde, ya roƙi gwamnatin Oyo ta dakatar da shirin tsige shi
- Oba Oyerinde ya ce Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin sarauta, Ademola Ojo, ya umarci a fara neman sabon Sarki
- Sarkin ya ce wasu kotuna sun riga sun yanke hukunci kan batun, don haka ya nemi gwamnatin Oyo ta hana ci gaba da shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Surulere, Oyo - Sarkin Aresaadu na Iresaadu da ke ƙaramar hukumar Surulere a Oyo, Oba Abraham Adeyeye Oyerinde, ya roƙi gwamnatin jihar Oyo.
Basaraken ya bukaci a dakatar da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Ademola Ojo kan shirin cire shi a sarauta.

Source: Facebook
Sarki ya zargi shirin tsige shi a Oyo
Sarkin ya ce Ojo na ƙoƙarin cire shi daga matsayin Aresaadu na Iresaadu ba bisa ƙa’ida ba, duk da akwai umarnin kotu da ke ci gaba da aiki, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya
Oba Oyerinde ya ce Kwamishinan ya rubuta wasiƙu biyu, a watan Satumban 2025 da Satumban 2026, ga shugaban ƙaramar hukumar Surulere.
Ya ce wasiƙun sun nemi a fara tsarin neman wani ɗan takara domin nada shi a matsayin Aresaadu na daban, bisa zargin cewa hukuncin kotu ya soke nadinsa.
A cikin wata sanarwa, Oyerinde ya roƙi mukaddashin gwamnan ya dakatar da tarukan da shugaban ƙaramar hukumar Surulere da gidan sarautar Emiolu suka fara yi domin neman sabon ɗan takarar sarautar.
Ya ce babu wata kotun da ta bayyana kujerar Aresaadu a matsayin wadda ta zama babu kowa, saboda haka bai kamata a fara shirin nada wani sabon sarki ba.
Ya ce:
“Yana da matuƙar muhimmanci da gaggawa in sake jawo hankalinka kan wani lamari mai tayar da hankali da ya shafi rashin adalcin da ake yi mini.
“Wannan rashin adalci ya shafe ni a matsayina na Aresaadu na Iresaadu, Oba Abraham Oyerinde, daga Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta ƙarƙashin jagorancin Ademola Ojo.
“Ma’aikatar ta sake aika wasiƙa a watan Satumban 2026 ga shugaban ƙaramar hukumar Surulere, inda ta umarce shi ya nemi gidan sarautar Emiolu ya gabatar da ɗan takarar da za a nada a matsayin Aresaadu na daban, alhali har yanzu ina kan karagar sarautar.”

Source: Original
Sarki ya ce kotu ta yi hukunci kan rigimar sarautar
Ya ƙara da cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara, a cikin shari’ar CA/1/291/2002, ta yanke hukuncin cewa ba lokacin gidan sarautar Emiolu ba ne na gabatar da ɗan takara.
Sarkin ya ce daga baya gidan sarautar Emiolu ya shigar da ƙara mai lamba HOI/4/2019 domin kalubalantar nadinsa, amma an yi watsi da ƙarar ba tare da an ɗaukaka ƙara ba.
Oyerinde ya ce ya riga ya yi irin wannan koke a wata buɗaddiyar wasiƙa da aka wallafa a Tribune a ranar 28 ga Oktoba 2025, cewar Daily Post.
Gwamna Diri ya tsige Sarki a Bayelsa
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayar da umarnin tsige sarkin Ogboinbiri, Okosughe Benson Eseimokumo, tare da rushe majalisar sarakuna.
Wannan mataki ya biyo bayan rikicin ranar Talata da ya yi sanadin asarar rai da kone-kone a garin na Ogboinbiri da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu.
Tun kafin a sanar da tsige sarkin, gwamnatin Bayelsa ta sanya dokar ta-ɓaci ta awanni 12 domin dawo da zaman lafiya a garin da ake hako man fetur.
Asali: Legit.ng
