Yan Bindiga Sun Mamayi Mutane a Kananan Hukumomi 2, Sun Kashe Bayin Allah da Dama

Yan Bindiga Sun Mamayi Mutane a Kananan Hukumomi 2, Sun Kashe Bayin Allah da Dama

  • Yan bindiga sun kai hare-hare a kananan hukumomin Giwa da Kubau na jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyar
  • Daga cikin wadanda aka kashe akwai jami'an rundunar yan bijilanti ta jihar Kaduna (KadVS) guda uku
  • Maharan sun kuma sace mutane 27 tare da yin awon gaba da shanun al'ummar wasu yankunan yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Giwa da Kubau na jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu 27.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai jami'an hukumar yan bijilanti ta jihar Kaduna (KadVS) uku.

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa a karamar hukumar Giwa, yan bindigar sun kashe mutane biyu a garuruwan Tunburku, Tudun Amada da Kallon Kura, yayin da suka kashe jami'an KadVS uku a karamar hukumar Kubau.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tarwatsa mutane, sun maida garuruwa 15 kango a jihar Katsina

Shehu ya bayyana sunayen jami'an KadVS da aka kashe da Dallami Dantani, wanda shi ne mataimaki na biyu a rundunar KadVS ta Kubau, da Abdullahi Hamisu da Zakariyya Musa.

KadVS ta tabbatar da hare-haren

Jami'in hulda da jama'a na KadVS, Yunusa Shehu, ya tabbatar da hare-haren a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Shehu ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da shanun al'ummar yankunan a wasu hare-hare daban-daban.

Ya bayyana cewa yan bindigar sun kai hare-hare lokaci guda a Tunburku da ke gundumar Kidandan da Tudun Amada da ke gundumar Kadage da sanyin safiyar ranar Litinin.

A Tunburku, an kashe mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Alhaji Surajo da Alhaji Ado. A bangare guda kuma, yan bindigar sun yi garkuwa da mazauna Tudun Amada 26.

Wasu 'yan bindiga sun sace shanu

A wani harin daban, yan bindigar sun kutsa cikin kauyen Kura da ke gundumar Danmahawayi da misalin karfe 9 na dare, inda suka yi awon gaba da shanun wasu mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Wuta ta kama rigi rigi a fitacciyar kasuwa, an tafka asara mai yawa a jihar Kano

Bayan samun bayanan sirri kan motsin yan bindigar, jami'an KadVS sun bazama domin binsu da kuma kwato dabbobin, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani yana jagorantar taro a fadar gwamnatinsa Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun yi musayar wuta da yan bindigar, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya tare da barin shanun kafin su tsere.

Wata majiya ta tsaro ta ce jami'an tsaron sun kwato shanu 19 daga hannun yan bindigar da misalin tsakiyar daren ranar Asabar.

Yan bindiga sun tashi jama'ar kauyuka 100

Kun ji cewa mutanen kauyuka fiye da 100 sun rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga a wasu kananan hukumomin Kaduna.

Garuruwan da lamarin ya shafa na karkashin kananan hukumomi shida da suka haɗa da Shiroro, Kachia, Kajuru, Kagarko, Chikun da Birnin Gwari duk a jihar Kaduna.

Shugaban ƙungiyar mutanen Kudancin Kaduna, Tabara Kato, ya ce sama da kauyuka 100 ne aka raba da muhallansu, yayin da tsohon kakakin ƙungiyar, Luka Binniyat, ya ce adadin ya kai 245.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262