Wuta Ta Kama Rigi Rigi a Fitacciyar Kasuwa, An Tafka Asara Mai Yawa a Jihar Kano
- Gobara ta kama da daddare a kasuwar Kofar Wambai da ke jihar Kano, inda ta lalata shaguna, rumbunan ajiya da wasu gidaje
- Jami'in hulda da jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin
- Lamarin ya kara jefa damuwa kan yawaitar gobara a kasuwannin jihar Kano, inda 'yan kasuwa ke ci gaba da fuskantar asara sakamakon irin wadannan gobara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wata gobara da ta tashi cikin dare ta lalata shaguna, wuraren ajiya da gidaje shida a Kasuwar Kofar Wambai da ke jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma'a, 4 ga watan Satumba, 2026 a yankin Babban Layi, bangaren Yan Robobi da ke cikin kasuwar.

Source: Original
Jami'in hulda da jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwra lamarin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Gobara ta kama a kasuwar Kofar Wambai
Ya ce ce tawagar bayar da agajin gaggawa ta hukumar ta samu kiran neman dauki da misalin karfe 9:43 na dare daga P.Fi.S Usman Idris Fagge.
Ya ce jami'an kashe gobara daga hedkwatar hukumar da tashoshin Rijiyar Zaki, Sabon Gari, Gidan Gwamnati da Bompai sun garzaya wurin domin kashe wutar.
Abdullahi ya ce bayan isarsu wurin, sun tarar da wani bene mai hawa biyu, mai girman kafa 120 da 125, ya kama da wuta.
Ya ce:
“Ginin da ke dauke da shagunan robobi da wuraren ajiya ya yi mummunar konewa. Shaguna biyu da ke kasa, biyu a bene na farko, dakunan ajiya shida da kuma shaguna na wucin gadi guda hudu a saman bene sun kone.”
Gobara ta babbake gidaje a Kano
Ya ce gidajen da gobarar ta shafa sun hada da Gidan Alhaji Sani, Gidan Sani Muhammad, Gidan Alhaji Kwa Kwa, Gidan Alhaji Shafi’u da Gidan Alhaji Sulaiman.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar ya kara da cewa gobarar ta fara ne daga saman bene kafin ta bazu zuwa sassan da ke kasa.
Hukumar kashe gobarar ta tabbatar da cewa wata na'urar samar da wutar lantarki ta hasken rana da aka girka a ginin ce ta haddasa gobarar.
Ya ce jami'an kashe gobarar sun yi nasarar shawo kan wutar tare da hana ta bazuwa zuwa wasu sassan kasuwar.

Source: Facebook
Shugaban hukumar, Alhaji Sani Anas, ya bukaci 'yan kasuwa da mazauna yankin su kasance masu taka-tsantsan tare da daukar matakan kariya daga gobara.
Ya shawarce su da su sanya na'urorin gano gobara, su tanadi ingantattun na'urorin kashe wuta tare da tabbatar da bin ka'idojin kariya a kowane lokaci domin rage aukuwar irin wannan ibtila'i.
Gobara ta kama a gidan gwamnan Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa gobara ta tashi a gidan Gwamnan Zamfara Dauda Lawal da ke GRA a Gusau da misalin karfe 7:20 na daren Talata, 1 ga watan Satumban 2026.
Shugaban Hukumar Kula da Kashe Gobara ta Zamfara, Injiniya Bello Sani Gusau, ne ya jagoranci tawagar jami’an hukumar zuwa gidan gwamnan domin shawo kan gobarar.
Asali: Legit.ng

