Dattijo Mai Shekaru 87 Ya Yi Yunkurin Hallaka Alkali, Ya Sare Masa Hannu
- Rundunar ’yan sandan Adamawa ta gurfanar da dattijo mai shekaru 87 bisa zargin yunkurin kashe alkalin kotu
- Ana zargin shi da sare hannun alkalin, Dauda Hamman, da adda yayin da yake jagorantar shari’a
- Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a kotu, inda ya ce shaidan ne ya jefa shi cikin aikata laifin, sannan kotu ta tsare shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Rundunar ’yan sandan Adamawa ta gurfanar da wani dattijo mai shekaru 87, Dahiru Garba, bisa zargin yunkurin kashe alkalin kotun yankin Fufore.
An ce lamarin ya faru ne ranar 31 ga Agusta, 2026, a Kotun Yankin Mayo-Ine da ke karamar hukumar Fufore.

Source: UGC
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Suleiman Nguroje, ya fitar ranar Talata a Facebook, ya ce wanda ake zargin ya sare hannun alkalin.
Yadda dattijo ya sare hannun alkali
Rundunar ta ce Dahiru Garba, mazaunin kauyen Korawa, ya kai wa alkalin da ke jagorantar kotun, Hon. Dauda Hamman mummunan hari.
An ce dattijon ya yi amfani da adda wajen sare hannun alkalin sau da dama, lamarin da ya jawo masa munanan raunuka.
Lamarin ya faru ne yayin da alkalin yake jagorantar shari’ar da ke tsakanin wanda ake zargin da wani mutum mai suna Ismail Yusuf.
Bayan faruwar lamarin, jami’an ’yan sanda sun kama Dahiru Garba nan take, sannan aka fara gudanar da bincike kan zargin da ake masa.

Source: Original
Matakin da yan sanda suka dauka
Rundunar yan sanda ta ce an tura shari’ar daga hedikwatar ’yan sanda ta sashen Fufore zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Yola.
An tura shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka a ranar 4 ga Satumba, 2026, domin gudanar da cikakken bincike da gurfanar da wanda ake zargi.
An tuhumi Garba da laifin jikkata mutum mai tsanani, wanda ya saba wa sashe na 219 na dokar Penal Code ta Adamawa ta shekarar 2018.
Bayan an karanta masa tuhumar tare da fassara mata ma’anarta, wanda ake zargin ya amsa laifinsa a gaban kotun.
A yayin amsa laifin, Garba ya dora alhakin abin da ya aikata kan shaidan, yana mai cewa ya yi matukar nadamar abin da ya faru.
Bayan sauraron bayanan, kotun ta bayar da umarnin a tsare Dahiru Garba a gidan gyaran hali na Yola.
An bayar da umarnin tsare shi ne har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron shari’ar a wani zaman kotu na gaba.
Kwamishinan ’yan sandan Adamawa, Kabir Hassan, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta tabbatar da gudanar da shari’ar yadda ya kamata.
Yan ta'adda sun kai hari a Adamawa
A baya, an ji cewa mutane sun mutu bayan da ake zargin ’yan Boko Haram sun mamaye ƙauyen Zaranga da ke ƙaramar hukumar Gombi.
Wani mazaunin yankin ya ce an gano gawarwakin mutane, yayin da wasu da dama ke ci gaba da bacewa bayan harin.
Wani mazaunin Zaranga ya ce matarsa da wasu ’yan uwansa biyu suna cikin waɗanda aka kashe yayin harin.
Asali: Legit.ng

