Ana Maganar 2027, Sanata Bello Mandiya Ya Riga mu Gidan Gaskiya

Ana Maganar 2027, Sanata Bello Mandiya Ya Riga mu Gidan Gaskiya

  • Rahoto ya nuna cewa tsohon Sanatan da ya wakilci Katsina ta Kudu, Sanata Bello Mandiya, ya rasu a Abuja yana da shekaru 62 a duniya
  • Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana rasuwar tsohon sanatan a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya
  • Mandiya ya wakilci Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawa daga shekarar 2019 zuwa 2023, bayan ya taɓa zama Shugaban Ma’aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina – Tsohon Sanatan da ya wakilci Katsina ta Kudu, Sanata Bello Mandiya, ya rasu a Abuja ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2026, yana da shekaru 62 a duniya.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana matuƙar alhini da kaduwa kan rasuwar tsohon sanatan, yana mai cewa mutuwarsa babban rashi ce ga jihar da ƙasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalung ya jefawa Christopher Musa tambayoyi kan zargin Nasir El Rufa'i

Sanata Bello Mandiya
Marigayi Sanata Bello Mandiya. Hoto: Maiwada Danmallam|Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin ma'aikacin gwamnati mai kishin ƙasa wanda ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban Katsina da Najeriya.

Gwamna Radda ya bayyana rasuwar Mandiya a matsayin babban rashi musamman ga al'ummar Katsina ta Kudu da kuma 'yan siyasar jihar.

Radda ya ce rasuwar Sanata Mandiya ta girgiza shi matuƙa, yana mai cewa marigayin ya sadaukar da wani ɓangare na rayuwarsa wajen yi wa jama'a hidima.

Mukamin da ya rike a baya

Gwamna Radda ya tuna cewa Sanata Bello Mandiya ya taɓa zama Shugaban Ma’aikata ga tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari.

Daga baya ne aka zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa, inda ya wakilci mazabar Katsina ta Kudu daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Radda ya bayyana cewa ƙwarewar da Mandiya ya samu da kuma hidimar da ya yi a matakin jiha da tarayya na daga cikin abubuwan da za su kasance cikin gadon da ya bari.

Kara karanta wannan

Albashin wasu sojoji ya zarce Naira miliyan 2 duk wata a Najeriya

Ta'aziyya ga iyalan marigayin

Gwamna Radda ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, tsohon Gwamna Aminu Bello Masari, al'ummar Katsina ta Kudu da abokan siyasarsa.

Ya kuma jajanta wa abokansa da abokan aikinsa, da kuma tsoffin abokan aikinsa a Majalisar Dattawa ta 9 ta Najeriya.

Radda ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya saka masa da alherin da ya aikata, sannan Ya ba shi Aljannal Firdausi.

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayin da masoyansa ƙarfin jure wannan babban rashi.

Maiwada Dan Malam ya wallafa a Facebook cewa za a gudanar da jana'izar Sanata Bello Mandiya a Apo Legislative Quarters da ke Abuja da ƙarfe 11 na safiyar Talata.

Jaruma Zee Diamond Ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumar shirin Labarina, Zainab Diamond, wadda aka fi sani da Maman Bintalo, ta rasu bayan fama da doguwar jinya.

Rahotanni sun bayyana cewa jarumar ta rasu ne bayan sallar Asuba, inda abokai da masoyanta suka bayyana alhininsu tare da yi mata addu'ar neman gafara da rahama.

Masu juyayin rasuwar sun roƙi Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta da 'yan uwanta haƙurin jure babban rashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng