Dangote Ya Zabi Kasar da zai Kafa Sabuwar Matatar Mai a Afrika

Dangote Ya Zabi Kasar da zai Kafa Sabuwar Matatar Mai a Afrika

  • Aliko Dangote ya zaɓi tsibirin Lamu da ke gaɓar tekun Kenya a matsayin wurin da za a gina sabuwar masana'antar mai ta Gabashin Afirka
  • Babban jami'in kamfanin Dangote ya shaida cewa ginin zai ɗauki watanni 30 kuma masana'antar za ta iya sarrafa ganga 700,000 a rana
  • Rahotanni sun bayyana cewa Dangote ya gayyaci gwamnatin kasar Tanzania ta sanya hannun jari a aikin matatar da zai a yankin Lamu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Najeriya - An ɗage rudanin da aka dauki lokaci ana yi dangane da inda za a gina sabuwar matatar mai ta Gabashin Afirka ta Aliko Dangote, bayan wani babban jami'in kamfanin ya tabbatar da cewa za a kafa ta a tsibirin Lamu da ke Kenya.

Mataimakin shugaban harkokin mai da iskar gas a kamfanin Dangote, Edwin Devakuma ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa a Lamu ne aka yanke shawarar gina masana'antar.

Kara karanta wannan

Da gaske alkalin da ya ba Tinubu nasara a kotu a zaben 2023 ya makance?

Alhaji Aliko Dangote
Lokacin da Dangote ke magana a wajen taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wajen da Dangote zai yi matata

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Lamu tsibiri ne da yake gaɓar tekun Kenya, ƙasar da ke da mafi girman tattalin arziki a Gabashin Afirka.

An kiyasta za a gama aikin ginin nan gaba ɗaya cikin watanni 30, kuma matatar za ta sami ƙarfin sarrafa ganga 700,000 a rana.

Batun da aka yi kan Tanzania

Wasu rahotanni sun nuna cewa kafin a yanke hukunci a kan Lamu, an taɓa ɗaukar Tanzania ma a matsayin wuri mai yiyuwa.

A ƙarshen watan da ya wuce, Dangote ya wallafa a Facebook cewa ya ziyarci Tanzania ya kuma yi taro da shugabar ƙasar, Samia Suluhu Hassan.

A wannan taro, ya bayyana dalilin da ya sa aka zaɓi Lamu maimakon Tanzania, tare da gayyatar Tanzania ta sanya hannun jari a wannan babban aikin.

Haka kuma a baya Dangote ya bayyana cewa yana tunani ne kan birnin Mombasa da ke Kenya kafin a ƙarshe ya sanar da zaɓin Lamu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Ƙarfin matatar Dangote a Najeriya

Matatar Dangote da ke Najeriya, wadda ta fara aiki a shekarar 2024, ita ce mafi girma a nahiyar Afirka baki ɗaya tare da ƙarfin sarrafa ganga 650,000 a rana.

Kamfanin yana da shiri na ƙara ƙarfin masana'antar har zuwa ganga miliyan 1.4 a rana nan da shekarar 2028, wanda hakan zai mai da ita mafi girma a duniya baki ɗaya.

Masana'antar ta canza yanayin kasuwar mai a Najeriya bayan ƙasar ta dogara shekaru da shekaru wajen shigo da man fetur daga waje duk da ita ce ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu hakar mai a duniya.

Matatar Dangote da ke Lagos
Wani sashe na matatar Dangote da ke jihar Legos a Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Dangote bai rage kudin mai ba

A wani rahoton, mun kawo muku cewa jama'a na cigaba da korafi kan rashin karya farashin man fetur a Najeriya da matatar Dangote ba ta yi ba.

Hakan na zuwa ne bayan kasashe sun rage kudin litar mai bayan sanar da tsagaita wuta da Amurka da Iran suka yi ya karya farashin danyen mai.

Sai dai matatar Dangote ta yi martani da cewa ba ko yaushe farashin mai ya ke sauka idan haka tafaru ba, domin suna da tsohon kaya da aka saya da tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng