An Kama Gungun Barayi a Abuja, Wasu a kusa da Babban Masallacin Kasa
- Rundunar ‘yan sandan FCT ta kama mutane 10 da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati a wasu samame daban-daban da aka gudanar
- An kwato wayoyin lantarki da ake amfani da su wajen rarraba wutar lantarki, tare da wata fitilar titi mai amfani da hasken rana
- ‘Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike domin gano sauran mambobin kungiyoyin da ake zargi da aikata laifin da masu sayensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Rundunar ‘Yan Sandan FCT ta sanar da kama mutane 10 da ake zargi da lalata muhimman kayayyakin more rayuwa na gwamnati a wasu sassan Abuja.
Rundunar ta ce an kama wadanda ake zargin ne a ayyuka daban-daban da jami’an ‘yan sanda suka gudanar a Kubwa, Wuye da yankin Masallacin Kasa.

Source: Facebook
Rundunar 'yan sandan Abuja ta wallafa hotunan wasu daga cikin mutanen da aka kama a wata sanarwa da wallafa a shafinta na Facebook.
An kama barayi 5 a Kubwa
A ranar 2 ga Satumba, 2026, da misalin karfe 6:00 na yamma, tawagar sintiri daga ofishin ‘yan sanda na Kubwa ta hango wasu mutane suna lalata wayoyin lantarki a yankin Bazango-Kubwa.
Jami’an sun kama mutanen biyar da ake zargi da aikata laifin, wadanda su ne Goodname Oriarebun, mai shekaru 29; Timothy Donald, mai shekaru 28; Ayo Buli, mai shekaru 26; Emmanuel Elijah, mai shekaru 28; da Christian David, mai shekaru 28.
An kama wani a Wuye
Haka kuma, tawagar sintiri daga sashen ‘yan sandan Wuye ta kama wani mai suna Moses Luka, yayin da ake zarginsa da tono wayoyin lantarki a hanyar da ke tsakanin Magic Land da filin wasan Abuja.
‘Yan sanda sun ce an kama shi ne a yayin da ake zargin yana aikata laifin.
A wani samame daban, tawagar leken asiri daga sashen ‘yan sandan Wuse ta kama wasu mutane hudu a yankin Masallacin Kasa.
Wadanda aka kama su ne Musa Abdullahi, Suleiman Idris, Aliyu Isa da Muhammed Abdulrahman.
Rundunar ta ce an kama su ne bayan an sare wata fitilar titi mai amfani da hasken rana, a kokarin lalata ta da cire wasu daga cikin kayayyakin da ke cikinta.

Source: Original
Binciken 'yan sanda na ci gaba
Rundunar ‘yan sandan ta ce tana ci gaba da bincike domin gano tare da kama sauran mambobin kungiyoyin da ake zargi da aikata irin laifin.
Ta ce binciken zai kuma mayar da hankali wajen gano wadanda ke karbar kayayyakin gwamnati da ake sacewa ko lalatawa.
Dukkan wadanda ake zargin suna tsare a hannun ‘yan sanda, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
An samu jarirai a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan FCT ta ceto jarirai biyu da aka yi watsi da su a wasu wurare daban-daban a Kurudu da Gwagwalada, Abuja, bayan samun rahoton mazauna yankunan.
Rundunar ta ce lamarin farko ya faru ne a ranar Laraba, 2 ga Satumba, 2026, da misalin karfe 5:30 na yamma a Obodo da ke Kurudu, inda wani mazaunin yankin mai suna Innocent ya ji kukan jariri.
‘Yan sandan sun ce Innocent ya je duba inda kukan yake, inda ya gano wani jaririn namiji da aka nade cikin zani tare da sanya shi a cikin kwali aka yi watsi da shi.
Asali: Legit.ng


