Kwana 3 da Rasuwar Babban Basarake, an Nada Sabon Sarkin Gumel na 17

Kwana 3 da Rasuwar Babban Basarake, an Nada Sabon Sarkin Gumel na 17

  • Gwamnatin Jigawa ta mika ta’aziyyarta ga iyalan sarautar Gumel da al’ummar masarautar bayan rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II
  • Gwamna Umar Namadi ya amince da nada magajinsa a matsayin Sarkin Gumel na 17, bayan shawarar masu naɗa sarauta
  • Sabon Sarkin Gumel ya gaji mahaifinsa, wanda ya rasu bayan shekaru 46 yana mulkin masarautar, kuma ya taba zama Daraktan Tsaron Intanet na NITDA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gumel, Jigawa - Gwamnatin Jigawa ta sake mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan sarautar Gumel, al’ummar masarautar Gumel, Majalisar Sarakunan Jihar da dukkan al’ummar Jigawa.

Gwamnatin ta bayyana cewa tana tare da al’ummar jihar a wannan lokaci na babban bakin ciki, sakamakon rasuwar Mai Martaba Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II.

An nada sabon Sarkin Gumel a Jigawa
Sabon Sarkin Gumel, Lawan Ahmed Muhammad Sani da marigayi mahaifinsa da ya rasu. Hoto: Malam Bala Ibrahim.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar wanda aka wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Amurka ba za ta cafke Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya'

Gwamnatin ta roki Allah SWT Ya gafarta masa zunubansa, Ya karbi ayyukan alherinsa, sannan Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

Nadin sabon Sarkin Gumel

Bisa shawarar masu naɗa sarki na Majalisar Masarautar Gumel da Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, Gwamna Umar A Namadi ya amince da nadin sabon sarki.

Gwamnan Jigawa, Malam Dr. Umar A Namadi, FCA, ya amince da nadin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17.

Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani zai gaji mahaifinsa, Mai Martaba Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, wanda ya rasu ranar Alhamis, 3 ga Satumba 2026.

Marigayin ya rasu bayan ya shafe shekaru 46 yana mulkin masarautar Gumel, inda ya yi mulki mai cike da daraja da hidima ga al’ummarsa.

Kafin nadinsa a matsayin Sarkin Gumel, Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani ya kasance Chiroman Gumel, sannan ya rike mukamin Daraktan Tsaron Intanet a NITDA.

Martanin Gwamna Umar Namadi na Jigawa

Kara karanta wannan

"Musulunci ya yi rashi," Sarkin Musulmi ya shiga alhini bisa rasuwar Sarki mai martaba a Najeriya

Gwamna Umar Namadi ya nuna godiya ga masu naɗa sarki na Majalisar Masarautar Gumel, karkashin jagorancin Wazirin Gumel, Alhaji Adamu Muhammad Nasoro.

Ya kuma gode wa sauran mambobin majalisar bisa irin gudunmawarsu da rawar da suka taka wajen gudanar da tsarin zaben sabon sarkin.

Gwamnan ya kuma yabawa Sarakunan Hadejia, Kazaure, Ringim da Dutse, wadanda suke cikin Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, saboda shawarwarin da suka bayar.

Ya bayyana cewa shawarwarin sarakunan sun taimaka matuka wajen tabbatar da an gudanar da tsarin zaben sabon Sarkin Gumel cikin nasara.

A madadin gwamnatin Jigawa, Gwamna Namadi ya taya sabon Sarkin Gumel murnar samun wannan matsayi na jagorancin masarautar Gumel.

Gwamnan ya yi masa fatan samun shekaru masu yawa na nasarar gudanar da hidima ga Masarautar Gumel da kasa baki daya.

An yi jana'izar Sarkin Gumel a Jigawa

Mun ba ku labarin cewa dubban al’ummar Gumel da wasu sassan Najeriya sun taru a Juma’a domin halartar sallar jana’izar marigayi Sarkin garin.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Gwamnan Jigawa Umar Namadi, sarakuna da manyan ’yan siyasa sun halarci jana’izar.

Marigayi sarkin, wanda ya rasu yana da shekaru 85 a Alkahira, ya bar ’ya’ya 33, maza 21 da mata 12, da jikoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.