'Yan Ta'adda Sun Kai Kazamin Hari a Adamawa, an Rasa Rayukan Bayin Allah

'Yan Ta'adda Sun Kai Kazamin Hari a Adamawa, an Rasa Rayukan Bayin Allah

  • Rahotanni sun ce mutane sun mutu bayan da ake zargin ’yan Boko Haram sun mamaye ƙauyen Zaranga da ke ƙaramar hukumar Gombi
  • Wani mazaunin yankin ya ce an gano gawarwakin mutane, yayin da wasu da dama ke ci gaba da bacewa bayan harin
  • Wani mazaunin Zaranga ya ce matarsa da wasu ’yan uwansa biyu suna cikin waɗanda aka kashe yayin harin da sanyin safiyar ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Akalla mutane 11 ne aka rawaito cewa sun mutu a bayan da ake zargin ’yan Boko Haram sun kai a Adamawa.

'Yan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a ƙauyen Zaranga da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin ƙauyen ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta waya da jaridar The Punch ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

Sai dai mazaunin ya nemi a ɓoye sunansa saboda bai samu izinin yin magana da manema labarai a madadin hukumomi ba.

Ya ce ’yan Boko Haram sun mamaye ƙauyen da sanyin safiyar Litinin, inda suka fara harbe-harbe tare da ƙona gidaje.

An gano gawarwaki mutane 11

A cewar mazaunin, zuwa lokacin da yake magana, an riga an gano gawarwakin mutane 11 da aka kashe.

Ya ce har yanzu akwai wasu mazauna ƙauyen da ba a san inda suke ba, yayin da jami’an tsaro da ƙungiyoyin da ke gudanar da aikin ceto ke ci gaba da neman su.

“A yanzu, an gano gawarwaki 11. Mutane da yawa har yanzu sun ɓace. Ƙungiyoyin bincike da jami’an tsaro suna cikin daji suna neman mutanen da suka ɓace,” in ji shi.

An kashe matar wani mazaunin ƙauyen

Wani mazaunin Zaranga ya kuma bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa da wasu ’yan uwansa biyu.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya

Ya ce an kashe su ne yayin da ’yan Boko Haram suka mamaye ƙauyen da sanyin safiyar Litinin.

“Matata da wasu ’yan uwa na biyu su ma suna cikin waɗanda aka kashe yayin mamayar ƙauyena da sanyin safiya,” in ji mazaunin.

Harin ya ƙara tayar da fargaba a tsakanin mazauna yankin, musamman ganin cewa wasu mutane har yanzu ba a san inda suke ba.

’Yan sanda ba su tabbatar da harin ba

An yi ƙoƙarin samun tabbaci daga rundunar ’yan sandan jihar Adamawa kan harin.

An kira kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, sau da dama domin jin matsayar ’yan sanda kan lamarin, amma bai amsa kiran wayar ba.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, kakakin rundunar bai mayar da martani kan kiran wayar da aka yi masa ba.

Saboda haka, adadin mutanen da suka mutu da kuma alhakin harin ba su samu tabbaci daga hukumomin tsaro ba a lokacin da aka wallafa rahoton.

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Adamawa
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Janar Musa ya ce an yi galaba kan 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan taaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce gwamnatin tarayya ta yi galaba kan ta’addanci a Najeriya.

Janar Musa ya ce hare-haren ’yan ta’adda ba su kai tsananin da suka kasance a baya ba, yayin da matsalar garkuwa da mutane ta fi bayyana a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng